07.29.2020 - By Sarewa Radio
Matsalar fyade, matsala ce da ta zama ruwan dare musaman a arewacin Najeriya, inda a yan kwanakin nan rahotanni suka yawaita akan fyade musamman ga kana nan yara maza da mata har ma da jarirai. Saboda haka ne a cikin wannan shirin muka gayyato Fakhriyya Hashim 'Yar rajin kare hakkin mata tare da Saratu G Abdullahi, Malamar Jinya da kuma rajin kare hakkin mata domin tattaunawa akan wannan matsala. Asha sauraro lafiya.