Shirin Kasuwa a kai miki dole tare da Faruk Yabo a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matsalar karancin sabbin kudin da babban bankin Najeriya CBN ya sauyawa fasali ya haddasa tarnaki ga harkokin yau da kullum baya ga tsayar da hada-hadar kasuwanci, dai dai lokacin da wata jita-jita ke cewa babu takardun da za a buga sabbin kudaden ko da ya ke Madab'ar kasar ta ce ta na da wadatattun takardun buga kudin sai dai rashin umarnin bugawar daga bankin na CBN.