Yau dai muna yawan kwaikwayon mutane na abubuwa da suke yi ba tare da la'akari da rayuwarmu a matsayin mu na musulmi ba. Kama daga yadda muka murnar bukin aure, haihuwa har da ma baqin cikin na mutuwa. Wai ko muna tunanin yadda musulmi ya kamata ya tafiyar da al'amuran sa? A taqaice, Mal. Abbas da Mal. Zahruddeen sun bayyana mana wani muhimmin al'amari a wannan Podcast din.