
Sign up to save your podcasts
Or


IYALI SU NE GINSHIƘIN AL’UMMA; IDAN GIDA YA GYARU, AL’UMMA MA ZA TA SAMU GYARA.
GINA IYALI NAGARI BA YA TSAYAWA GA SAMUN KUƊI KO ZAMA TARE KAWAI, A’A, YANA BUƘATAR SOYAYYA, FAHIMTAR JUNA, MUTUNTA JUNA, HAƘURI, AMANA DA KYAKKYAWAR TARBIYYA.
A YAU ZA MU TATTAUNA MUHIMMAN RUKUNAN DA AKE BUƘATA WAJEN GINA IYALI NAGARI, DA KUMA WASU ƘALUBALEN DA KAN KAWO RASHIN JITUWA TSAKANIN MA’AURATA DA SAURAN ’YAN UWA.
BABBAN BAƘO: MAL. LAWAN ADAM GIGINYU, MASANIN KIMIYYAR ZAMANTAKEWA A NAKJERIYA.
MAI GABATARWA: DR. SANI MOUSSA MAGAWATA.
“Shugabanci na Gari a Tsarin Dimokuraɗiyya.” Shugabanci ba mulki kawai ba ne, illa amana ce, nauyi ne, da kuma hidima ga jama'a. A tsarin dimokuraɗiyya, ana bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu, amma tambayar ita ce: ta yaya za mu tabbatar da cewa wannan zaɓe yana haifar da shugabanci mai adalci, gaskiya, amana da bin doka? A yau za mu duba ginshiƙan shugabanci na gari, rawar shugabanni da jama'a, da kuma manyan ƙalubalen da ke hana samun kyakkyawan shugabanci a Najeriya da Afirka.
A yau mutane da dama suna son su zuba jari domin su ƙara samun kuɗi, amma rashin ilimi yana sa wasu su yi asara ko kuma su faɗa cikin hanyoyin da ba su dace ba.
A wannan shiri na Rumfar Africa Podcast Hausa, kashi na (55) za mu tattauna muhimman ƙa'idojin da ya kamata kowane mai son zuba jari ya sani, tare da ƙwararren masani a fannin tattalin arziki, zuba jari da Islamic Finance, Dr. Nabil Bello Sa'id, Manajan Darakta na Konooz Investments.
Ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshe, domin wataƙila wannan tattaunawa za ta canja yadda kuke kallon zuba jari baki ɗaya.
Domin neman karain bayani a Konooz Investments:- +2347063829915 | +2349069968666 | +2349015995200
MATASA DA SON YIN KUƊI A GAGGAUCE: HANYAR ARZIKI KO TARKO?Domin yin nazari a kan wannan batu, muna tare da babban baƙonmu, Farfesa Munir Abdullahi Kamba, wanda zai yi mana bayani kan tushen wannan matsala, illolinta, da kuma hanyoyin da matasa za su bi wajen gina arziki cikin hikima da dorewa.
Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya?
-------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene ne mafita? Kuma wane tasiri wannan rikici zai iya yi ga tattalin arzikin duniya, tsaron ƙasashe, har ma da rayuwar al'ummar Afirka?
A wannan shirin na Rumfar Africa Podcast Hausa, za mu yi nazari cikin natsuwa tare da baƙo na musamman domin fahimtar tushen rikicin, matsayinsa a siyasar duniya, da hanyoyin da za su iya kai ga zaman lafiya.
TAKAITACCEN SHARHI A KAN ABINDA KE WAKANA A KASHEN SAHEL, TARE DA MASANIN KIMIYYAR SIYASA DA SHA'ANIN MULKI
Da’awar Musulunci da Bible: Hanyoyin Isar da Saƙon Musulunci ga Mabiyan Kiristanci.Ta yaya Musulmai za su yi da’awa cikin hikima da fahimtar addinin Kirista? Wane matsayi Bible take da shi a tattaunawar addinai? Kasance tare da mu domin jin tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin gina fahimta, mutunta juna da kuma isar da saƙon Musulunci cikin basira da hikima.
“HAJJI: MAKARANTAR SHUGABANCI”
Shin wane darasi shugabanni da al’umma za su koya daga hajji? Ta yaya hajji ke koyar da tsari, adalci, tawali’u da haɗin kai?
Domin tattauna wannan batu, muna tare da babban bako:IMAM, DR. MUHAMMAD SULAIMAN ADAM.
Sana’ar Jari Bola ta zama ɗaya daga cikin sana’o’in zamani da suka mamaye duniya, tana jan hankalin miliyoyin mutane saboda damar samun riba cikin gajeren lokaci. Amma a bayan nasara akwai ƙalubale, haɗari da dabarun da ke buƙatar ilimi da ƙwarewa. A wannan shiri na musamman, za mu tattauna kan nasarorin sana’ar, ƙalubalen da masu ita ke fuskanta, hanyoyin inganta ta a wannan zamani, da kuma yadda ake gudanar da sana’ar jari bola a sassa daban-daban na duniya. Kasance tare da babban bako, Aliyu Sabo Yakasai, fitaccen mai sana’ar jari bola, domin jin sirrika, gogewa da muhimman darussa masu ɗaukar hankali!
A WANNAN KASHI NA 49, MUN TATTAUNA YAKIN KWANAKI 12 TSAKANIN ISRA’ILA DA IRAN:
• ASALIN RIKICIN.
• TARIHIN KAFUWAR ISRA’ILA DA IRAN.
• YADDA DANGANTAKA TA DIFLOMASIYYA TA RIKIDE ZUWA GABA DA ADAWA.
• ME YA TAYAR DA RIKICIN YANZU.
• RAWAR KASASHEN YAMMA WAJEN TALLAFAWA ISRA’ILA.
• DA TASIRIN RIKICIN A NAHIYAR AFRIKA.
TARE DA BABBAN BAKO: DR. RIYA’UDDEEN ZUBAIR MAITAMA — ƘWARARRE A KIMIYYAR SIYASA DA SHA’ANIN MULKI, KUMA MALAMI A JAMI’AR BUK KANO.
SHIRIN NA CIKE DA BAYANAI MASU ZURFI DA FAHIMTAR ABUBUWAN DA KE FARUWA A DUNIYAR SIYASA.
#podcastclips #Hausa #duniya #siyasa
From the publisher's feed