Hausa Fatwa

Hausa Fatwa

Download on the App Store

Hausa Fatwa episodes

  • Fatawowin Rahama: Q&A 27-09-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar Lahadi 16/4/1446- 27/9/2026


    Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_


    1. Hukuncin ba da umurni ( prompt) ga Artificial Intelligence (“AI”) ya sa hotuna mutane suna aiwatar da umurnin da ake so su aiwatar!


    2. Hukuncin cin allowance da ake bawa mai Hidimar ƙasa (NYSC) da ba ya zuwa wajen aikin da aka sa shi yayi (primary assignment).


    3. Hukuncin yin Sallah a massallacin da ba a kiran Sallah!


    4. Ya hallata mutum ya kar6i bashin da Moniepoint suke bayarwa!


    5. Ana iya taya mai azumin kaffara in ya gaji?


    6. Maganin Kambun Baka!


    7. Hukuncin shan Maganin ƙarfe (Tauri)


    8. Tsawon wanne Lokaci ne mutum zai zauna ba tare da iyalansa ba!


    9. Hukuncin Sallah da gajeran wando!


    10. Hukuncin wanda in ya ta shi neman aure a ce masa ga irin sunan matar da zai aura bisa ilimin taurari!


    11. Akwai hadisin da ya ce mace mai aure tafiyarta daga daki zuwa kitchen ta na da ladan umrah ?


    12. Hukuncin sana’ar siyar da karnuka?


    13. Hukuncin mamu da yayi dariya ana tsaka da Sallah!


    14. Hukuncin gyara ƙabarin wanda ba musulmi ba!


    15. Akwai hadisi da Annabi ﷺ ya ambaci mutane dubu 70 da za su shiga aljanna ba tare da hisabi ba?


    16. Akwai fifiko tsakanin sahun gaba a Sallah da sahun baya?


    17. Hukuncin wanda yayi Sallah da najasa a tufafi?

    53 min
  • Fatawowin Rahama: KU KASANCE MASU GASKIA - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar Asabar 15/4/1446-26/9/2026


    Shimfida: _Ko Kusance Masu Gaskiya Tare Da Masu Gaskiya_


    Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    Tambayoyi da Amsoshi :


    1. Menene hukuncin shimfiɗa darduma ta hanya mai dauke da hoton Ka’aba ko wata alama da take nuna alqiba?


    2. Meye sa mutane suke rubata Abdulrahma da “L” maimakon Abdurrahman!


    3. Hukuncin ‘yan Kasuwa ma su sa kaya a hanya da wurin amfanin mutane gaba ɗaya!


    4. Za a iya yiwa gawa wanka a banɗaki!


    5. Mutum zai iya koyan Al-qur’ani ta hanyar sauraro a cassette?


    6. Hukuncin masu amfani da takardun wasu domin samun aiki?


    7. Ya hallata mutum ya karanta Al-ƙur’ani ba tare da riga ba!


    8. Ya hallacin albashin kwanaki da mutum ya yi ƙarya ya ɗauke su da uzurin ƙarya!


    9. Mutumin da ya rabu da matarsa, zai iya karbar wasu daga cikin kayan Lefen da ya bata!


    10. Menene ma’anar karya mace a Hadith Annabi (ﷺ)


    11. Hukuncin nannade kaya in mutum zai yi Sallah?


    12. ⁠Menene hukuncin sana’ar da wasu mata ke yi, inda suke sanar da cewa gobe za a yi awara ko makamancinta, Ana biyansu kafin suyi

    54 min
  • Fatawowin Rahama: Q&A 19-09-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar Asabar - 8/4/1448 - 19/9/2026


    Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_


    1. ​ Menene bambancin tsakanin Sallar Shuruq da Sallar Walaha!


    1. ​ Idan mamu ya samu raka’a uku tare da na gefe da shi, in ya tashi cikawa, na gefensa zai iya bin shi su cika tare?


    1. ​ Shin matar da take al’ada za ta shiga massallaci? In ta shiga za ta iya taba mushafi?


    1. ​ Hukuncin addu’a buƙata bayan Tahiyar ƙarshe!


    1. ​ Ya hallata iyaye su hana ‘ya’yansu aure ba wani dalili?


    1. ​ A daidai ina Ladan zai ce mutane su yi Sallah a gida in ana tsaka da ruwan sama?


    1. ​ Bambancin yanke Sallah da Sallamar fita daga Sallah!


    1. ​ Shin addinine ko al’ada - amare ba za su fita daga gidan aurensu ba har sai wani lokaci?


    1. ​ Matar da mijinta ya saketa saki biyu-kafin ta gama iddarta sai ya rasu- za ta yi masa takaba?


    1. ​ Hukuncin Sallah da Singeleti!


    1. ​ Za a iya bawa wanda ya mallaki nisanin Zakka, Zakka?


    1. ​ Mutumin da yake da lokacin da yake fitar da zakka, sa ya samu kyautar kuɗi a wani lokaci na daban , zai hada wannan kyautar a lissafin zakkarsa a lokacin da ya saba?


    1. ​ Hukuncin wanda yake cikin damuwa akan laifin da yayi duk da ya tuba!


    1. ​ Wanda yayi Umra sannan yake son ya sake yiwa wani, A ina zai ɗauko harama?
    54 min
  • Fatawowin Rahama: Q&A 13/08/2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar - Lahadi 2/4/1448 - 13/9/2026


    Tambayoyi da Amsoshi tare da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    1. Sakin da ake kome da sakin da ba a kome


    2. Dole mace ta sanya hijabi in za ta yi aikin gida a tsakar gidan da akwai makwabta da suke bene za su iya hangota ta tagarsu?


    3. Menene hukuncin kwanciyar rub da ciki!


    4. Soja da aka tura shi aikin tsaro tsakanin Nigeria da Chadi na tsawon shekara ɗaya zai iya ƙasaru Sallolinsa a iya tsawon zamansa?


    5. Shin zihari ne mace ta kira mijinta ‘yaya’ ko shi ya kirata ‘ƙanwata’


    6. Mutum da ya tuno ana binsa ba shi bayan mutuwar wadanda suke bin shi bashi?


    7. Hukuncin mace da aka cire mata da a cikin mahaifa, za ta cigaba da ibada?


    8. Mutumin da yake son yin ibada amma shaidan yake masa wasuwasi cewa ba don Allah yake yi ba!


    9. Hukuncin kallon fuskar mace yayin cinikaya!


    10. Hukuncin fitsarin mace a tsaye!


    11. Hukuncin wanda yayi Atishawa Liman ya na huɗuba!


    12. Ana rama nafilar rawatib ta bayan Magriba in ya kubce ma mutum!


    13. Idan aka hada Sallar Magriba da Isha, za a yi ratibin Sallar Magriba?


    14. Ya hallata wanda suke Sallah a wajen sana’arsu, su hada Sallah sannan su cigaba da sana’oinsu?


    15. Menene madogarar masu kiran Sallah kafin lokaci!


    16. Da mutum yayi bara da ya nemi rancen kudi da ruwa, wanne ya fi laifi?


    17. Yaya mutum zai yi mu’amala da mahaifiyarsa mai mu’amala da bokaye!


    18. Yaya mace za ta yi da mijinta mai yawan “chatting” da mata?


    19. Ya hallata mutum ya nemi a siya masa mota saboda ya inganta sanarsa; ya burge mutane da yake harka da su!


    20. Yin sallah a hotel da ke kusa da Harami daidai yake da sallah a massallacin Harami?

    53 min
  • Fatawowin Rahama: NASIHA GAME DA ZAƁE - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Asabar 1 /4/1448 - 12/9/2026


    Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    Shimfida : Nasiha ga Al’uma game da Zaɓe da Waɗanda za a Zaɓa!

    Tambayoyi da Amsoshi:


    1. In mutum ya ta shi daga bacci da Asuba, dole sai yayi wanka kafin yayi Sallah?

    2. hukuncin walimar haihuwa!

    3. Direba ya na tuƙa mota sai wani ya buge shi, sanadiyar hatsari ya rasu ( wanda ya dake mai motar)!

    4. Hukuncin ma’akacin da in an aike shi sayo kaya, sai yake ƙara kuɗin akan yadda ya sayi kaya!

    5. Matafiyi zai iya haɗa Sallallin da ake haɗasu yayi su a ƙasaru; sannan in ya je massallacin ya bi liman, ya cika Sallah?

    6. Matafiyi zai iya yin Rawatib!

    7. Mutum da ya yiwa Mace ciki sannan ya aureta daga baya, ɗan da aka samu zai ci gado?

    8. Yaya iddar matar da tayi ɓari bayan kwana biyar da rasuwar mijinta

    9. Wanene maraya a Musulunci

    10. Yaya matsayin wanda bai yi nafila bayan Ɗawafi saboda ba a Sallar nafila bayan La’asar.

    11. Wace irin cuta ce take zama annobar da take ɗaukar hukuncin annoba a sharia!

    53 min
  • Fatawowin Rahama: ADDININ MUSULUNCI BAYA KARƁAR BIDI’A - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawoyin Rahma


    Ranar Asabar - 23/3/1448H – 5/9/2026


    Tara da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON


    Shimfiɗa: Addinin Musulunci Ba Ya Karɓar Bidi’a


    Tambayoyi da Amsoshi:


    1. Wanda ya yi Istikhara, amma ya kasa cire son yarinyar da ya yi Istikharar a kanta daga zuciyarsa; menene hukuncin Istikhrarsa?


    2. Hukuncin amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar bidiyo daga hotunan mutane domin sarrafa su.


    3. Hukuncin yawan mafarkin mutuwa ga mace mai juna biyu.


    4. Shin ya halatta mutum ya bawa Makocinsa Kirista aron abin hawa domin zuwa coci?


    5. Mene ne hukuncin bashin da Gwamnatin Najeriya take bin ɗalibi har ya mutu bai samu aiki ba?


    6. Shin ya kamata a yi jam’i na biyu a masallacin da yake da limami Ratibi?


    7. Hukuncin matan da suke cire mayafi a wuraren bukukuwa a gan DJs!


    8. Hukuncin wanda yake fama da lalura, ta yadda duk lokacin da ya yi tsarki sai wani abu ya fito daga gabansa.


    9. Mene ne hukuncin taimaka wa ɗalibai wajen satar amsa don kar su faɗi Jarrabawa?

    53 min
  • Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawowin Rahma


    Ranar Lahadi


    17/3/1448 - 30/8/2026


    Tambayoyi tare da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*


    1. Wacce hanya mutum zai bi ya zama ɗalibin ilimin hadisi!


    2. Wanda ya samu raka’a ta ƙarshe a Sallar Magriba, yaya zai kammala Sallarsa?


    3. Hukuncin wanda ya rikice ya kasa tuna raka’a nawa yayi?


    4. Lamarin wadda in za ta yi Sallah sai ta ji kamar wani abu zai faɗo mata?


    5. Hukuncin mutuwa a wurare masu falala?


    6. Laifin wanda ya taimaka wajen zubar da ciki dai dai yake da wanda ya kashe wanda aka haifa?


    7. Mutum zai iya yafewa wanda yake bi bashi da ya mutu ba sai ya fadawa iyalan mamacin ba?


    8. Ya hallata mutum yayi sadaqa ga iyayensa da suka rasu!


    9. Yaya mutum zai sa riba ga kayan da yake sayarwa!


    10. Idan aka gina coci a Fili ba tare da izininsa mai filin ba, yaya magada za su yi?


    11. Sallar ƙasaru ga matafiyi!


    12. In mutum zai cutu a hanyar sa ta zuwa massallaci, zai iya Sallah a gida sannan kuma ya samu ladan wanda ya je massallaci?


    13. Mamu zai iya ƙin bin liman da ya hada Sallah in mamun yana ganin sharuɗɗan haɗa sallolin ba su cika ba?


    14. Yaya hukuncin Tela da yake aiki a shagon da wutar lantarki da aka janyo zuwa shagon ta sata ce?


    15. Akwai addu’ar rufe gida ko daki?


    16. Ana iya tofi da shafawa yaro yayin yi masa addu’a safe da yamma?


    17. Mace za ita iya Sallah da zani da hijabi da ya rufe jikinta, ko da bata da riga?


    18.kashin kaji najasa ne?


    19. Hukuncin mutumin da aka bawa bashi da riba amma yake musun haka?


    20. Hukuncin Wucewa gaban mamu ta kofar da aka bar ta a bude domin wucewar mutane!


    21. Mace za ta iya Sujjadar Tilawa ba tare da hijabi ba?


    22. Mutum zai iya azumin domin ya samu lada sannan ya rage kiba?


    23. Mutumin da yayi alwala, yayi Azkar din bacci sannan ya sadu da iyalansa, sai ya sake Azkar?


    24. Mutumin da yake Sallar dare, an ina ya kamata yayi addu’oinsa?


    25. Yaya ya kamata musulmi ya gaishe da manya?


    26. Akwai hadisin da ya ce za a fara sahu daga tsakiyar sahu?

    53 min
  • Fatawowin Rahama: BACIN AQIDAR ‘HUMANITY’ - Prof. Sani R/Lemo

    FATAWOYIN RAHMA


    Ranar Asabar


    16/3/1448H – 29/8/2026


    _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_


    Shimfiɗa – ```Bacin Aqidar “Humanity”``


    Tambayoyi da Amsoshi -


    1. Menene hukuncin neman ruwa daga wurin wanda ba Musulmi ba domin yin alwala.


    2. Shin mutum zai iya yin addu’a a Tahiya ta farko?


    3. Menene matsayin addu’ar da ake yi bayan Tahiya?


    4. Menene hukuncin fitar maziyyi ga mai azumi?


    5. Mutumin da ya samu sallar jana’iza bayan an riga an yi kabbara ta farko ko ta biyu, daga wace kabbara zai shiga cikin sallar?


    6. Menene hukuncin matafiyin da ya haɗa Sallar Azahar da La’asar a lokacin Sallar Azahar?


    7. Menene hukuncin matafiyin da bai yi Sallar Azahar a ƙasaru ba har sai da ya dawo gida a lokacin Sallar La’asar? Shin zai yi Sallar Azahar a ƙasaru ne ko cikawa zai yi?


    8. Mutumin da ya karɓi kuɗin ɗan’uwansa, bayan rasuwarsa, shin zai iya amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen hidima ga iyalinsa, bisa hujjar cewa yana mayar da haƙƙin mamaci!


    9. Menene hukuncin mutumin da yake karɓar albasa daga wanda suke zama tare, wani lokaci ya mayar, wani lokaci kuma ba ya mayarwa?


    10. Menene hukuncin mutumin da yake yin Sallah a cikin shagonsa, kuma ba ya zuwa Sallar Jam’i?

    53 min
  • Fatawowin Rahama: Q&A 9-8-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    *Fatawoyin Rahma*


    Ranar Lahadi


    25/2/1448 - 9/8/2026


    Tambayoyi da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*


    1. Hukuncin Dillanci!


    2. Mutumin da yake so wata, ita ma take sonsa, amma iyayensa ba sa son su tare; yaya zai yi?


    3. Hukuncin wanda ya ci abinci yana azumi da mantuwa!


    4. Hukuncin yin kyauta ga ma’akacin Immigration da yayi aikin yin passport ga mutumin da ya masa kyauta!


    5. Hukuncin rage shekaru don a daɗe a na aiki?

    6. Hukuncin kiwon dabbobi domin siyarwa Kiristoci lokacin bukkunansu!


    7. Ya hallata mutum ya bibiyi ma’aikatu domin bankaɗo cin hancin da rashawa?


    8. Hukuncin ta da iƙama bayan Kiran sallah-ba tare da tazara ba.


    9. Yaya hukuncin tube mace tumbur a mata tiyata!


    10. Hukuncin yara da ba sa turawa mahaifinsu kuɗi saboda ya na da kuɗi kuma mahaifiyar su ta umurce su da ka da su ta ra masa!


    11. Ta yaya mutum zai bambance jarabawar da Allah ya masa saboda laifinsa da kuma jarabawar da Allah ya yi masa domin daukakar darajarsa!


    12. Dole ne mutum ya san ma’anar adduar da ya ke yi?


    13. Yaya ake yin Istikhara?


    14. Za a yi salatin Annabi ﷺ a sallar nafila?


    15. Wanda ya mutu ta hanyar nitsewa a ruwa ko gobara, za a masa wanka?


    16. Shawara ga mai fama da matsanancin wasuwasi?


    17. Hukuncin wanda yayi ƙarya akan halayyar wani mutum!


    18. Yaushe ake “ as-sallatu khairul minannaum”?


    19. Falalar Limanci?


    20. Ana yin azumin kaffara ga wanda ba musulmi ba?


    21. Hukuncin Jami’an tsaron da suke hana wanda aka tsare yin sallah!


    54 min

About Hausa Fatwa

From the publisher's feed

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.