VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2]
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri.USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga.USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafin soji da Amurka ke baiwa gamayyar sojojin da Saudiya ke jagoranta a yaƙin Yemen.Nigeria Elections 2019: Manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya, sun sake jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla.Nigeria: Gwamnar jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsallake rijiya da baya a ƙauyen Lugumanu*."Mu mun ɗauka sojoji ne, ashe ba sojoji ba ne. Suna da kayan sarki kuma dukansu sun more..."Ba shirin Domin Iyali.