BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG) [1][2]
Hosts: Badriya Tijjani KalarawiIndia: 'Yan sanda Indiya sun ce mutane sha bakwai ne suka mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Delhi.Haiti: Masu zanga-zanga sun yi ta ƙona tayoyi a titunan ƙasar Haite tare da jefan jami'an tsaro da duwatsu.Nigeria: Wasu 'yan Najeriya sun ce sun gaji da alƙawarin da gwamnati ke musu na bunƙasa harkar sufurin jirgin ƙasa a sassan ƙasar."Muna jin daɗin yanda aikin kasancewa. Amma kuma abinda muke gude shine, kada yazo ya kasance kamar aikin bayan ya fara kuma a tsaya. Sabida, sun san abu kamar za su yi, za su yaudari mutane. Can kuma, su yi amfani da kuɗin su yi wani abu."Labarin wasanni <> sports.Nigeria Elections 2019: Za ku ji zargin da jam'iyyar APC da PDP ke yi kan kawowa juna hare-hare gabannin zaɓen da ke tafe a Najeriya.