Sign up to save your podcasts
Or

Send us a text
A yayin da al’ummar Kirista a sassa daban-daban na ƙasar nan ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala, da annashuwa da haɗuwa da iyalai, akwai kuma waɗanda wannan lokaci ya zo musu cikin ƙunci da jimami.
Waɗannan su ne mutanen da matsalolin tsaro—kamar hare-hare da rikice-rikice—suka tilasta musu barin gidajensu da muhallansu. A maimakon shagulgula a cikin gidajensu, suna gudanar da bikin ne a sansanonin gudun hijira, inda rayuwa ta cika da ƙalubale, da rashin isasshen abinci, da tsaro da kulawar jin ƙai.
Wannan bambanci na nuna yadda bukukuwan Kirsimeti ke zuwa wa ‘yan ƙasa da yanayi daban-daban—ga wasu na farin ciki, ga wasu kuma na juriya da fatan samun mafita.
Irin halin da Martha Andrew ta tsinci kanta a ciki kenan a unguwar Kudansa dake karamar hukumar cikun dake jihar Kaduna.
Zamu ji irin halin da wannan baiwar Allah ta tsinci kanta a ciki da ma wasu dake sansanin ‘yan gudun hijiran a cikin shirin na yau.
By Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah IbrahimSend us a text