
Sign up to save your podcasts
Or


Send us Fan Mail
Yayin da ake gudanar da bukukuwar Mauludi a sassa daban daban a garuruwan kasar nan, wasu yankunan na da tasu bukukuwar ta daban.
Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ake gudanar da bikin sallar Gani.
Send us Fan Mail
’Yan Najeriya da dama ne dai da suka yi ilimin zamani dole ta sa suka rungumi sana’o’in da a baya ake ganin na kaskantattu ne don su samu na sakawa a bakin salati.
Mai yiwuwa hakan ne ya sa wasu, musamman matasa, suka yanke kauna da cewa shafe lokaci ana karatun kan iya taimaka wa mutum magance bukatunsa nay au da kullum.
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Send us Fan Mail
A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.
Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.
Send us Fan Mail
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Send us Fan Mail
Sau da dama wadanda ke dauke da nau’in jini na AA na bayyana cewa sun fi kowa lafiya.
Suna bayyana cewa basa rashin lafiya kamar yadda masu sauran na’ukan jini ke yi.
Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan ko da gaske ne masu nau’in jini na AA sun fi sauran masu nau’ukan jini lafiya.
Send us Fan Mail
Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati.
Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan da aka tura su.
Send us Fan Mail
A Jamhuriya ta Hudu a Najeriya, wadda ta fara a shekarar 1999, an samu sauye-sauye masu yawa a bangaren tattalin arziki da harkokin kuɗi, ciki har da tasowar bankunan Musulunci. Wannan tsari na banki ya samo asali ne daga buƙatar samar da hanyoyin mu’amala da kuɗi da suka dace da koyarwar addinin Musulunci, wato hanyoyin da ba su ƙunshi riba, da zamba, ko rashin tabbas ba.
A farkon lokaci, ra’ayin kafa bankunan Musulunci ya fuskanci muhawara da adawa daga wasu ɓangarori na al’umma, musamman saboda fahimtar da ake yi cewa tsarin na da alaƙa da addini. Sai dai daga bisani, gwamnati da hukumomin kula da harkokin banki, musamman Babban Bankin Najeriya (CBN), sun samar da dokoki da ka’idoji da suka bai wa bankunan Musulunci damar aiki a matsayin bankunan da basa cin riba.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne akan tasowar bankunan musulunci da kalubalen da suke fuskanta.
Send us Fan Mail
Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa.
Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance.
Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin.
Ko mece ce gaskiya game da amfani da wannan iri na GMO?
Send us Fan Mail
Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.
Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Send us Fan Mail
Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma.
Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya.
Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
From the publisher's feed
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.