Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

By Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah IbrahimNewsNews CommentaryPolitics
Download on the App Store

Najeriya a Yau episodes

  • Yadda Cutar Zazzabin Lassa Ke Kisa Da Hanyoyin dakile Ta

    Send us Fan Mail

    A yayin da Najeriya ke fuskantar kalubale daban-daban a fannin lafiya, cutar zazzabin Lassa ta sake ɗaga kai a wasu jihohin ƙasar. Cutar wadda ake dangantawa da berayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar, tana yawaita ne musamman a lokutan sanyi zuwa farkon damina, lamarin da ke jefa al’umma cikin fargaba a kowace shekara.

    Rahotanni daga hukumar dake hana yaduwar cututtuka ta Najeriya sun nuna cewa tun daga farkon shekarar 2026, an samu daruruwan mutane da suka kamu da cutar a jihohi fiye da goma sha huɗu, tare da mace-mace da dama. Jihohi irin su Bauchi State, Ondo State, Taraba State da Edo State na daga cikin wuraren da cutar ta fi yin kamari.


    Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, alkaluma sun nuna cewa 2025 ta samu yawan masu kamuwa da cutar fiye da yadda aka fara gani a 2026, sai dai masana sun nuna damuwa kan yadda mace-mace ke iya ƙaruwa sakamakon jinkirin kai marasa lafiya asibiti.

    Shin me ke haddasa wannan yawaitar a kowace shekara? 

    Wadanne hanyoyi za a bi wajen magance ta?


    Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi kokarin amsawa.

    20 min
  • Yadda Ake Kamuwa Da Basir Da Hanyoyin Magance Ta

    Send us Fan Mail

    Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.

    A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta.

    Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta.

    Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.

    27 min
  • Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki

    Send us Fan Mail

    Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma.


     Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki baya bukata.
     A takaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na kwakwalwar sa.


     Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan alakar dake akwai tsakanin yin azumi da kuma lafiyar jikin mutum. 

    30 min
  • Falalar Bude Baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi

    Send us Fan Mail

    Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma.


     Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci.
     Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada.


     Shin ko mene ne matsayin bude-baki tare da iyali a watan Ramadana?
     Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da bude baki tare da iyali yake da shi.

    27 min
  • Me Nadin Sabon Sufeton 'Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya?

    Send us Fan Mail

    Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), matakin da ya sake jawo hankalin al’umma kan makomar tsaro da gyaran harkokin rundunar ‘yan sandan ƙasar nan. Naɗin sabon jagoran rundunar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ciki har da satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan ƙasa.


    Sabon Sufeton ana sa ran zai ɗora kan nasarorin da aka samu a baya tare da kawo sababbin tsare-tsare da dabarun da za su ƙarfafa yaƙi da laifuka, inganta hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma, da kuma farfaɗo da martabar rundunar. 

    Ko ta yaya wannan naɗin sabon shugaban ‘yansandan zai amfani tsaron cikin gida Najeriya?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    19 min
  • Shin Da Gaske An Fara Samun Ɓaraka Tsakanin Atiku Abubakar Da Peter Obi A Tafiyar ADC?

    Send us Fan Mail

    Rahotanni daga sassa daban-daban na siyasar Najeriya na nuna cewa ana fara samun ɓaraka a tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar tafiyar ADC, musamman tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.


    Ko da yake har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da wannan saɓani, majiyoyi na nuni da cewa sabanin ra’ayi kan jagoranci, tsarin tafiya, da kuma makomar zaɓen 2027 na iya zama tushen wannan rikici.
    Wasu masu sharhi na ganin cewa irin wannan saɓani abu ne da kan taso a duk wata haɗaka ta siyasa, musamman idan manyan ‘yan takara masu farin jini suna ƙoƙarin haɗa kai domin cimma buri ɗaya. Sai dai tambayar ita ce: shin wannan ɓaraka za ta iya raunana haɗakar kafin ta kai ga gaci, ko kuwa za a samu sulhu a tsakaninsu?


    A yau, shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan gaskiyar lamarin, me ke haddasa wannan jita-jita, da kuma irin tasirin da hakan zai iya yi ga makomar siyasar Najeriya.

    21 min
  • Falalar Sallan Tarawih Ga Alummar Musulmi A Watan Ramadan

    Send us Fan Mail

    A duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kama, al’ummar Musulmi kan cika masallatai domin gudanar da sallar Tarawihi cikin karsashi da himma. A kwanakin farko, ana ganin sahu sun cika, zuciya cike da nishadi da kwadayin lada. Sai dai abin takaici, bayan wasu kwanaki, wasu kan fara ja da baya — wani saboda gajiya, wani saboda shagaltuwa da harkokin yau da kullum, ko kuma rashin juriya.


    Wannan yanayi na nuna bukatar tunatarwa kan muhimmanci da falalar sallar Tarawihi, domin ita ba kawai karin ibada ba ce a watan Ramadan, illa wata babbar hanya ce ta neman gafara da kusanci ga Allah. Manzon Allah (SAW) ya karfafa tsayuwar dare a watan Ramadan, yana mai bayyana cewa duk wanda ya tsaya sallar dare cikin imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba ne kan falalar sallan tarawihi yayin da Musulmi ke cigaba da gudanar da azumin watan Ramadan.

    18 min
  • Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta

    Send us Fan Mail

    Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su.


     Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama.


     Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan dake sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya.

    25 min
  • Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba

    Send us Fan Mail

    A duk lokacin da watan azumi ya zo, Musulmai da dama sukan karɓe shi da murna da shauƙi, suna shirya ibada da ƙara kusanci da Allah. Sai dai ga wasu, musamman masu fama da larurar gyambon ciki wato ulcer, watan azumi kan zo da wani yanayi na damuwa da fargaba. Yayin da wasu ke jin daɗin azumi, su kuma suna cikin ƙalubalen yadda za su iya jure yunwa da ƙishirwa ba tare da cutar ta tashi ko ta jawo musu matsananciyar wahala ba.


    Ciwon ulcer na haddasa zafi a ciki, tashin zuciya, amai ko jin ƙuna musamman idan ciki babu komai na tsawon lokaci. Wannan ne ya sa azumi, wanda ke buƙatar jure yunwa daga asuba zuwa magariba, kan zama babban ƙalubale ga masu fama da wannan larura. Wasu kan kasa yin azumi gaba ɗaya, yayin da wasu ke fara shi amma su kasa kammalawa saboda tsananin ciwo.


    Ko ta wadanne hanyoyi ne masu fama da wannan larurar zasu bi wajen yin azumi ba tare da sun sha wahala ba?

    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kai.

    19 min
  • Yadda Muka Yi Asarar Miliyoyin Naira A Kasuwar Singa Muna Ji Muna Gani

    Send us Fan Mail

    ‘Yan kasuwa da dama a jihar Kano sun kwana sun tashi da juyayi da alhinin gobara da ta faru ta kuma lashe musu dimbin dukiyarsu suna ji suna gani ba tare da sun iya tabuka komai ba.


    Gobarar da ta tashi a kasuwar singa dake jihar Kano, ta fara ne da misalin karfe 4:30 na ranar asabar ta kuma cigaba da ci har zuwa wayewar garin ranar lahadi. Wannan gobara ta yi sanadiyyar raba ‘yan kasuwa da dama da hanyar cin abincin su, inda ta jefa su da iyalansu cikin halin kunci.


    Ko wanne irin hasara wadannan ‘yan kasuwa suka tafka sakamakon wannan gobara?

    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    18 min

About Najeriya a Yau

From the publisher's feed

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.