Hausa Newsletter

Kanun Labaran Hausa na Alhamis 2026-03-19


Listen Later

BBC Hausa Safe

* Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra’ila ba za ta sake kai hari kan cibiyar samar da iskar gas ta South Pass da ke Iran ba.

* Manyan jami’an leƙen asirin Amurka sun shaidawa wani kwamitin majalisar dattawan ƙasar cewa kusan makonni uku (3) da soma yaƙin Iran har yanzu shugabancin ƙasar na nan daram.

* A Najeriya, wasu mutane da suka samu raunuka yayin tashin bamabaman da aka samu a baya-bayan nan a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun shaida wa BBC yadda lamarin ya faru:

* “Muna shiga shi ke nan bom ya tashi. Na faɗi, yarinyata ma ta faɗi. Ta faɗi shikenan ba rai. Kan ta wannan a nan ya fashe.”

* “Sun shigo ne da mashin. Su uku ne a ciki har da direban. Sai suka wurga mun kwalba. Bam ɗin ne a ciki.”

* A jihar Kano da ke Najeriya, ɓangaren sarki na goma sha biyar (15) a jihar Kano Aminu Ado Bayero sun bayyana janye aniyar su ta fita hawan salla ƙarama:

* Wannan ba daidai ba ne. To amma mu tunda muna kotu babu abinda zamu ce sai mu ƙara haƙuri. Na tabbata da izinin Allah ya yi hawan ƙarshe. Amina Ado Bayero shi zai ci gaba da hawa har kuma sanda Allah ya karɓi ran mu gabaɗaya in Allah ya so ya yarda.

DW Hausa Safe

Full show <> gabaɗayan shirin:

Host <> mai gabatarwa: DW Hausa’s Muntaqa Ahiwa.

* Halin da al’ummomin Jamhuriyar Nijar ke ciki game da tsadar makamashi yayin da ake shagulgulan ƙarmar salla a yau Alhamis a kasar.

* Ƙungiyar tuntuɓa ta Dattawan Arewa Najeriya ACF kuwa ta yi kira ne ga shugaba Bola Tinubu da ma dukkanin ƴan Najeriya su miƙe tsaye domin dakatar da matsasolin tsaro da ke addabar Najeriya.

* Za kuma mu je yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo muku rahoto akan yaƙin da ke haifar da matsaloli masu yawa a halin yanzu a ƙasar Iran.

* Saudiya ta ce tana da ƴancin ɗaukar matakin soja bayan wani hari da aka kai.

* Tarayyar Turai ta ƙi amincewa buƙatar shugaban Amurka Donald Trump na sa baki a yaƙin Iran.

* Sarki Charles na Birtaniya ya yaba dangantakar da ke tsakanin Najeriya da ƙasarsa.

RFI Hausa (Ƙarfe 5 GMT na 2026-03-18)

Mai gabatarwa: RFI Hausa’s Ruqayya Abba Kabara

* Dubban mutane sun yi dandaso a Iran don ta’aziyyar ko kuma jana’izar manyan jami’an tsaron ƙasar Isra’ila da ta halaka.

* Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman gwamnati da su ajiye muƙamansu kafin ranar talatin da ɗaya (31st na Maris) ga watan da muke ciki.

* Mahukunta a Kenya sun yi dokar bai wa mata ma’aikatan gwamnati hutun kwanaki biyu (2) na al’ada.



This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com
...more
View all episodesView all episodes
Download on the App Store

Hausa NewsletterBy Hausa Radio News Headlines