Hausa Newsletter

Kanun Labaran Hausa na Asabar 2026-03-14


Listen Later

2026-03-14

BBC Hausa

Shirin Safe (2:00am EST)

* Shugaba Trump ya ce Amurka ta kai hare-hare a kan abin da ta kira wurare na soja a tsibirin Kharg, babbar tashar fitar da man Iran a tekun Fasha. (Labari mai alaƙa: DWHausa Safe #6)

* Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla ma’aikatan lafiya goma sha biyu (12) aka kashe a wani hari da Isra’ila ta kai kan wani a ƙaramin asibiti a kudancin ƙasar.

* Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, ta gargaɗi ƴan ƙasar musamman a jihohin Arewa game da yiwuwar ɓarkewar cutar sanƙarau yayin da aka fara shiga yanayin tsananin zafi.

* Ƙwayar cutar da ta fi sa sankarau din annoba shine ake samu mafi yawan ci a kusan arewacin Najeriya. In haka ya faru, sai mu yi ta bawa mutane ƙanana-ƙananan shawara na kar su [???]. Ba wani cunkoso, a dinga buɗe windo, sannan mu dinka sa mutane suna ɗan wanke baki da drip.

* (A filin Gane Mini Hanya) Har wa yau a Najeriya, majalisar dattawan ƙasar ta ce za ta sake gayyatar shugabancin kamfanin mai na ƙasar: NNPC, kan yadda wasu maƙudan kuɗaɗe suka yi ɓatan dabu a tsakanin shekarar ta 2017 zuwa 2023.

* Yaya ma za a yi a ce tiriliyan ɗari biyu da goma (210T) sun ɓace ko an rasa su, ba a bamu ƙididdiga da ta gamsar da mu ba? A ina kuka kashe su? A me kuka kashe?

* Mai gabatarwa: BBC Hausa Muhammad Annur Muhammad

DW Hausa

Shirin Safe (2:30am EST)

* Mai gabatarwa: DW Hausa Mohammed Tijjani Hassan

* (A shirin Sharhunan Bayan Labarai) A Najeriya, wata cibiyar samar da zaman lafiya ta horas da masu bukata ta musamman kan matakai da hanyoyin da za su bi domin kare kansu a yanayin rashin tsaro da kuma faɗace-faɗace.

* Yayin da a gefe guda, kungiyoyin kare muhalli suka fara gangamin wayar da kan al’umma domin dakile ambaliyar wato ambaliyar ruwa a arewacin Nijeriya.

* A Nijar kuwa sabuwar taƙaddama ce ta kunno kai a tsakanin gwamnati da shugabannin ƙasashen Turai kan buƙatar da suka sake miƙawa ta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum wanda ake tsare da shi yau kusan shekaru biyu.

* A Ghana kuwa za a ji ƙarin bayani kan wani tsari da aka samar wanda ya tanadi kare yara daga hatsarin da ke tattare da haƙar ma’adinai ta bayan fage wato Galamsey.

* Trump ya ce Iran ta faɗi a yaƙi kuma a yanzu haka tana son a cimma yarjejeniya. (Labari mai alaƙa: BBCHausa Safe #1)

* An kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke Iraqi a wannan safiya ta Asabar.

* Wani gagarumin harin Rasha ya yi ajalin mutane biyu a yankin Kiev na Ukraine.

2026-03-13

RFI Hausa

Labaran RFI Hausa na ƙarfe 5 na yamma agogon Najeriya da Nijar 13-03-2026… • RFI Hausa

* Mai gabatarwa: RFI Hausa Shamsiyya Haruna

* An ji ƙarar fashewar abubuwa masu yawa a tsakiyar birnin Tehran dai dai lokacin da ake ci gaba da ƙidayar waɗanda suka mutu a Isra’ila sakamakon harin Iran.

* Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince a sayi ƙarin makamai na zamani domin ƙarfafa gwiwar sojojin ƙasar wajen yaƙi da ƴan ta’adda.

* Senegal na sake nazartar yarjejeniyoyin haƙar iskar gas da man fetur da ƙasar ta ƙulla da kamfanonin ƙasashen waje.

BBC Hausa

Shirin Safe (2:00am EST)

Me ya sa magana kan yaƙin Isra’ila da Iran ta zama laifi a Najeriya?[13][14]

* Ƙungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS da nuna bangaranci wajen kama masu bayyana ra’ayansu akan yakin na Amurka da Isra’ila da suke yi da Iran a Najeriya.

* Salo ne da yake nuna cewa ana nuna kamar bambanci a tsakanin ‘yan Najeriya. Zaka ga cewa akwai waɗanda suke sukan ɗaya ɓangaren da ake yaƙi da shi amma ba ka taɓa ji an kama wani a cikinsu ba. Kaman nan gaba ɗayansa a arewacin Najeriya ake yin sa.



This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com
...more
View all episodesView all episodes
Download on the App Store

Hausa NewsletterBy Hausa Radio News Headlines