
Sign up to save your podcasts
Or


Mun tattauna da wani mai fashin bakin al'amuran ci gaba a kasashen duniya Adamu Hamza Bamalli. Inda ya fayyace mana hikimomin da ake amfani da su wajen kawo ci gaba a kasa, ciki har da maganar siyasa a kasashen duniya da ma namu kasashen.
Dakta Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.
Na sami tattaunawa Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban tawagar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya a 2023 da ke tafe. Ya bamu labarin kuruciyarsa har zuwa girma da shiga fagen siyasa, da ma dalilinsa na janye wa daga takarar shugabancin Najeriya don mara wa Atiku Abubakar baya.
Na'ima Idris Usman (Girls Talk Series), cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriya da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta, da kuma yadda ta je shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka na Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da YALI.
Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy mawaki ne, dan wasan kwaikwayon zahirin rayuwa da ya fito a tauraron wani shirin wasan talbijin a Amurka mai suna 90DayFiance wanda ake bibiyar saurayi da budurwa don ganin yadda alakarsu ta soyayya ke tafiya.
Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Niger a Najeriya, wacce ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo.
An karrama Halima Ali Shuwa da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa’o’inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil’adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta.
Adamu Garba II matashi ne mai kwarin gwiwa sannan wanda ya ke dan kasuwar da yayi iliminsa a tsakanin Najeriya har zuwa Amurka. Yana daga cikin 'yan takarar Shugaban Kasar Najeriya a shekarar 2023 mafi karancin shekaru a tsakanin masu neman wannan kujera a kasar da ta fi kowa ce kasar Afirka yawan al'umma da kuma karfin arzikin man fetur. Shine kuma wanda 'yan uwa da abokan arziki suka tara wa sama da naira miliyan 80 don yin takarar tasa a jam'iyyar APC amma kwatsam sai ya canja sheka zuwa YPP.
Mu'awiya Said Abdullahi, ya yi karatu ne a fannin zanen gidaje da kuma tsara birane a takanın Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria da wasu jami’o’in kasar Malaysia da kuma Koriya ta Kudu, inda yanzu haka ya ke aiki a matsayin shugaban bangaren kula da bangaren tsara birane a wani babban kamfani a birnin Seoul.
Ibrahim Sherif bakano ne dan Najeriya da ya bar gida tun yana dan saurayi zuwa Birtaniya domin aikin sa kai. Inda daga baya ya nausa Afirka ta Kudu inda ya cika burinsa na zama matukin jirgin sama, har ma ya buge da tsere keke a can.