Farfesa Abba Zubair Chedi na asibitin Mayo Clinic da ke Amurka, dan asalin jihar Kano ne a Najeriya da ya yi kaurin suna a Amurka, musamman a lokacin da ya shiga binciken yadda za a yi amfani da kimiyyar kwayar halitta ta 'stem cell' wajen kirkirar sassan jikin bil'adama, kamar zuciya da huhu don dasa wa mutanen da sassan jikin ya lalace ba tare da jiran sai wani ya mutum a cire a saka wa wani ba.