Hausa Newsletter

VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17


Listen Later

Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri

* US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka.

* US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya.

* Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel.

* Nigeria: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dad'in dangantaka da shugabannin majalisar dokokin k'asar a wa'adin mulkin sa na farko, da ya ce ya kawo cikas a harkokin mulki. Sai dai masu kula da lamura suna cewa wannan shi ne demokradiya.

“Ai aikin majalisa, d'aya daga cikin manya-manyar ayyukan shi ne ta taka birki ga b'angaren zartasuwa. Kuma duk wanda ya ke taka maka birki, ba lalle bane a ce ra'ayinku yana tafiya dai-dai kuma ana samun jittuwa a ko wane lokaci.”

* Taraba: Muna kuma da rahoto kan cigaba da jami'an tsaro suke samu a jihar Taraba a yunk'urin shawo kan masu garkuwa da jama'a.

* Sai kuma shirin Lafiya Uwar Jiki da Hauwa Umar ke gabatarwa.

Links:

* Stream or download: https://www.voahausa.com/a/4901612.html

* Permalinks: http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517

* Subscribe to the podcast here: https://pod.link/1278112963

* Tweet:



This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com
...more
View all episodesView all episodes
Download on the App Store

Hausa NewsletterBy Hausa Radio News Headlines