Barka Da Warhaka

Barka Da Warhaka

By Sarewa RadioSociety & Culture
Download on the App Store

Barka Da Warhaka episodes

  • Barka Da Warhaka: Episode 8 Balkisu Aliyu Mai Kilishi

    Kilishi, wani abincine na kasaita a kasar Hausa, wanda yake da sunaye daban daban misali a turanci ana kiransa da "Beef Jerky". Kasan cewar Amurka bata bari a shigo da nama Hausawa mazauna yammacin duniyar na fama da rashin Kilishi, Hakan yasa Balkisu Aliyu mai kamfanin Alsutra Kitchen ta fara yin Kilishin ana saida shi a kasashe da dama. Hakan yasa muka gayyato ta shirin Barka da Warhaka don tattaunawa da ita.

    1 hr 46 min
  • Barka Da Warhaka: Episode 7 Freiiboi

    A yau mun zanta ne da Sani TY Sha'aban wanda aka fi sani da Freiiboi mawaki dan shekaru 15, kan irin burin shi a rayuwa da kuma irin gatan da yasamu na tallafi da kuma kwarin gwiwa daga waurin mahaifinsa.


    53 min
  • Barka Da Warhaka: Episode 3 TY Sha'aban (Shaba)

    Ba 'boyayyen abu bane mafi yawancin iyaye basa tallafawa yaransu wajen kara musu kwarin gwiwa a bangaren wasanni da hikimomi na yau da gobe. TY Sha'aban wanda aka fi sane da (Shaba) ya bambamta da sauran iyaye domin kuwa shi yana tallafawa dansa (Freiiboi) wajen yin wakokin zamani. Ko me yasa? ku biyo mu cikin shirin Barka da Warka domin jin dalili.

    1 hr 29 min
  • Barka Da Warhaka: Episode 2 Matsalar Fyade

    Matsalar fyade, matsala ce da ta zama ruwan dare musaman a arewacin Najeriya, inda a yan kwanakin nan rahotanni suka yawaita akan fyade musamman ga kana nan yara maza da mata har ma da jarirai. Saboda haka ne a cikin wannan shirin muka gayyato Fakhriyya Hashim 'Yar rajin kare hakkin mata tare da Saratu G Abdullahi, Malamar Jinya da kuma rajin kare hakkin mata domin tattaunawa akan wannan matsala. Asha sauraro lafiya.

    2 hr 28 min
  • Barka Da Warhaka: Episode 1 Musgunawa Bakaken Fata

    A cikin shirin "Barka da Warhaka" kashi na farko mun gayyato Maryam Bugaje, 'Yar Jarida kuma mai fashin bakin akan lamuran yau da kullum inda muka tattauna game da zanga zangar da ta barke a Amurka sakamon cin zarafin bakaken fata da jami'an 'Yan sanda ke yi a Amurka.

    30 min
  • Barka Da Warhaka "Tallan Shirin"

    "Barka da Warhaka", shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra’ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga

    2 min

About Barka Da Warhaka

From the publisher's feed

Barka da Warhaka, shiri ne da ke sakarwa matasa linzamin bayyana ra’ayinsu a siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran batutuwan rayuwa ba tare da takunkumi ba. Zamani...riga