Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Ranar Masoya: 'Da Wuya A Samu Soyayyar Gaskiya A Yanzu'

    Ranar masoya kan dauki hankali a ranar 14 ga watan Fabreru, inda yawancin masoya ke kure malejin soyayyarsu.

    Amma akwai masu ganin ba lallai a samu soyayyar gasakiyaa yanzu ba. Sai dai ko kun san yadda aka yi wannan ta samo asali?

    Albarkacin ranar masoya Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba tasirin wannan rana da salsalar ta.



    27 min
  • Yadda ‘Yan Arewa Za Su Samu Kuɗi A Soshiyal Midiya

    Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu. 

    Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya  nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen  ganin sun amfana yadda ya kamata.



    27 min
  • Yadda Takura A Wajen Aiki Ke Ta'azzara Rayuwar Ma'aikaci

    A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba.

    Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadda za a warware damuwa a irin wannan yanayi.



    30 min
  • Matakan Kariya Daga Kwantawa Rashin Lafiya

    Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki.

    Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu.

    Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun da za su taimaka wajen ganin ba ku kwanta rashin lafiya ba.



    26 min
  • Yadda Wasan Kanawa Da Zagezagi Ya Samo Asali

    Abu ne da za a iya cewa sananne ga al’ummar Kano da Zazzau na tsokanar juna a tsakaninsu.

    Ana yawan taƙaddama kan shin wane ne mai gida tsakanin Kanawa da Zazzagawa.

    A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba tasirin wannan wasa tsakaninsu da kuma yadda ta samo asali.

    26 min
  • Matsalolin Da Suka Kewaye Kannywood

    Rade-radin matsaloli basa karewa dangane da masanaantar shirya finafinai ta Arewacin Najeriya mai cibiya a Kano Kannywood. 

    Shin mene ne abin da ke hana Kannywood cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya? 

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi boyayyun matsalolin da suka dabaibaye Kannywood. 

    30 min
  • Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri?

    Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna.

    Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa.

    Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a kan matakin da ake kai na bincike kan harin.

    26 min
  • Abin Da Zai Faru Idan Mutum Ya Cika Cin Goro

    Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo.

    Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a yankin.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa masu cin goro basu iya dainawa da kuma abin da masana suka ce zai iya faruwa idan cinsa yayi yawa.

    29 min
  • Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai

    Da zarar an ambaci wasiyya sai mutum ya fara tunanin mutuwa, ko wani abun na daban a rai.

    Wasu kan bar wasiyya ko da za su yi tafiya zuwa anguwa saboda gudun riskar wa'adi a lokacin da ba shiri. Shin ya mahimmancin wasiyya take da kuma tasirin hakan?

    Ku biyo mu shirin Daga Laraba na wannan makon domin jin mahimmancin barin wasiyya tun mutum na raye.

    27 min
  • Dalilin Da Maza Ke Haura Shekar 40 Babu Auren Fari

    Maza da dama na son aure amma kuma su kan ce fargabar ɗawainiya ta hana su. 

    Wasu kuma na cin karo da ƙalubale tun a wajen nema, lamarin da ya sa suke zarta shekarun samartakansu  ba aure. Toh shin da gaske ne abinda suke fada na cin karo da kalubale bayan aure

    Ku biyo mu cikin shirin Daga Laraba na wannan makon inda muka duba yadda wasu mazan kan shafe sama da shekara 40 ba aure.

    28 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…