Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Yadda 'Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai

    Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. 

    Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro.

    'Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon, bincike ne kan yadda ‘yan ta’adda ke amfani da albarkarun kasa na zinare wajen siyan makamai a yankin arewa maso yamma.

    29 min
  • Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya

    Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

    Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba. Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun bayyana wannan mataki a matsayin nuna son kai da kuma kokarin dakile sabuwar tafiya a cikin jam’iyyar.

    Wannan lamari ya sake haska yadda PDP ke ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda da yawa ke ganin zai iya shafar karfinta da hadinta kafin babban zaben da ke tafe.

    Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a kai.

    28 min
  • Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?

    Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya.


    Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi.

    Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya?


    Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

    28 min
  • Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci

    A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci.


     
     Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati.


     
     Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki.

    30 min
  • Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai

    Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa.


    Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar da ci gaba. 


    wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai shekara 65 bayan samun 'yancin kan Najeriya.

    31 min
  • Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

    Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.

     

    Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.

     

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.

    28 min
  • Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya

    A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. 


    Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.


    wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.

    30 min
  • Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku

    Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa. 


    A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa  yunkurin kashe kansa har sau uku. 


    ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ransa da kansa har sau uku?

    28 min
  • Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027

    Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027.


    A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu.

    22 min
  • Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo

    Wani sabon salo da wannan zamani ya zo da shi shi ne auren gwaji, inda mata kan yi shiga gidan miji da niyyar fita bayan wani lokaci.


    Sai dai manazarta suna cewa hakan ka iya haddasa matsalolin musamman idan mazajen auren ba su san da wannan shirin ba.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu mata suke yin auren gwaji.

    29 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…