Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Dalilan Zuwan Mafarautan Arewa Kudancin Kasar Nan

    Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu.


    A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta?


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa mafarautan arewa zuwa kudancin Najeriya yin farauta.

    31 min
  • Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah

    A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura.


    Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. 

    A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.

    27 min
  • Abin Da Kundin Tsarin Mulki Ya Ce A Kan Ayyana Dokar Ta Ɓaci

    A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar.


    Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari.
    Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar ya dauki wannan mataki, wasu kuwa cewa suke yi ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan ko Doka ta bai wa Shugaban Kasa ikon dakatar da gwamnan jiha da ma 'yan majalisar dokokinta?

    28 min
  • Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Kasar Hausa?

    Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa.


    Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma.
    Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo kwararo dauke da ganga da kayan kade kade suna bugawa suna waka.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan dadaddiyar aladar, don jin inda ta samo asali, tarihin ta, da kuma yadda ake Gudanar da ita.

    28 min
  • Yadda Zawarawa Suke Dandana Kuda A Watan Ramadana

    Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta.


    Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa.
    Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana.

    32 min
  • Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa

    A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”.


    A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. 
    Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.

    24 min
  • Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

    Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.

    Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma?

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.

    23 min
  • Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata

    Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban.

    A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba.
    Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar ’ya’ya maza a kan ’ya’ya mata.

    30 min
  • Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo

    Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. 

    A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.
    Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. 

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riko.

    24 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…