Gaskiyar Magana

Gaskiyar Magana

By Jamilah TangazaNews
Download on the App Store

All Gaskiyar Magana episodes

  • Tattalin Arzikin Arewa A Zaben 2027

    A yau na yi hira da Alhaji Babangida Lamido Kankarofi, masanin tattalin arziki kuma dan jam'iyyar APC wanda ya bayyana halin da tattalin arziki arewacin Najeria ke ciki a daidai lokacin da ake shirin zaben 2027. 

    13 min
  • Fa'idar Malaman Addini A Siyasa

    A yau mun yi hira da Dr Usman Ahmad, malami a Kwalejin koyar da shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano, dake Kano, dan jin ko laifi ne malaman addini su fitar da matsayinsu a lokacin zabe. 

    13 min
  • Dalilan Rashin Fita Jefa Kuri'a A Najeriya

     

    Shirin yau tattaunawa ce da Alhaji Umar Labaran Danga, dan siyasa, kuma mai sharhi kan siyasa da rayuwa a Nigeria inda ya ke haska mana dalilan karancin masu jefa kuri’a duk da yawan adadin masu rajista a kasar. 


     

    13 min
  • Yaya Jam'iyyun Adawa Ke Shirin Zaben 2027

    Zabe a kowacce kasa ba abu ne da ake masa rikon sakaina ba. Shin yaya jam’iyyaun adawar Nijeriya ke shirin Zaben 2027? A shirin mu na yau, mun tattauna da Hon. Abdullahi Dalhatu Dankano, dan jam’iyyar ADC. 

    13 min
  • Manyan Batutuwan Yakin Neman Zaben 2027

    Menene manyan batutuwan da suka sha kan al’umma a lokacin Zaben 2027? Shirin yau, kashi na biyu ne na hira da Dr Aminu Isma’ila Sagagi, malami a Jami’ar Bayero dake Kano, kuma mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya.

    13 min
  • Yaya Yakin Neman Zaben 2027 Ke Tafiya?

    Tattaunawa da Dr. Aminu Ismail Sagagi, malami a Jami’ar Bayero da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran rayuwa da siyasa, wanda ke bayyana damuwarsa kan salon yakin neman zaben 2027 da ake gani a Najeriya a yanzu. 

    13 min
  • Me Matasan 'Yan Siyasa Ke Cewa?

    An jima ana cewa tsoffin hannu sun mamaye siyasar Najeriya. Amma yanzu matasan kasar sun yunkuro. Sai dai yaya manufofinsu su ka banbanta da wadanda suke kalubalanta? Ga hira da Hon. Bello Babajo, shugaban jam'iyyar APM na jihar Adamawa.



    11 min