Kanun Labaran HausaRadio.net na BBC, DW, RFI, da CRI Hausa na 2026-05-15
Takaitattun kanun labaran Hausa daga BBC Hausa, DW Hausa, RFI Hausa, da CRI Hausa tare da timestamps, fassarar Turanci, da ƙarin mahada a HausaRadio.net.
Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-05-15
YouTube:
BBCHausa Safe
Mai gabatarwa: Ibrahim Yusuf Muhammad
🎧@0:14 Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin ƙulla yarjejeniyoyi da dama na kasuwanci da China yayin da yake kammala ziyararsa zuwa ƙasar.
🎧@0:24 Ukraine ta kai gagarumin hari ta sama a kan birnin Ryazan na ƙasar Rasha.
🎧@0:29 A Najeriya ana ci gaba da bayar da martani kan kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, cewa wa’adi ɗaya kacal zai yi idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, inda wasu ke ganin wannan magana ce kawai ta fatar baki.
🎧@0:52 A Jamhuriyar Nijar, hukumomi sun yi kira ga al’ummar ƙasar da su ɗauki matakan da suka dace domin guje wa fuskantar bala’o’i da aka sani sukan auku ne a lokacin damina.
BBCHausa Hantsi
Mai gabatarwa: Ibrahim Yusuf Muhammad
🎧@1:38 Shugabannin Amurka da na China na gudanar da ganawarsu ta ƙarshe yayin da Donald Trump ke kammala ziyararsa zuwa Beijing.
🎧@1:49 Firayim Minista na Birtaniya, Keir Starmer, na fuskantar ci gaba da matsin lamba daga jam’iyyarsa ta Labour.
🎧@1:56 A Najeriya, ‘yan sanda na jihar Bauchi sun ƙara haske game da wani mutum da aka kama ana zargin ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara tara fyade a garin Toro.
🎧@2:16 Har wa yau a Najeriya, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta fara wani shiri na musamman domin sauƙaƙawa masu fama da cutar tarin fuka samun magani cikin sauƙi.
🎧@2:47 Akwai kuma labaran wasanni a cikin shirin.
BBCHausa Rana
Mai gabatarwa: Umaima Sani Abdulmumin
🎧@3:20 Shugaba Trump na Amurka ya ce baya jin za a samu matsalar diflomasiyya ko yaƙi tsakanin ƙasarsa da China kan Taiwan.
🎧@3:30 Kafar yaɗa labaran Amurka ta ce gwamnati na shirin maka tsohon shugaban Cuba mai shekara casa’in da huɗu, Raúl Castro, a gaban kotu.
🎧@3:38 Jam’iyyar hamayya ta ADC a Najeriya ta ce ta shirya tsaf domin soma zaman tantancewa da neman mafita kan mutum ɗaya da zai mata takarar shugaban ƙasa.
🎧@4:04 Babban Bankin Najeriya ya yi gargaɗi cewa kuɗaɗen da ake kashewa gabanin babban zaɓen 2027 na iya sake jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki.
DWHausa Safe
Mai gabatarwa: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
🎧@5:02 Iran ta sanar da buɗe mashigar Hormuz ga jiragen dakon ruwan China a daidai lokacin da shugabannin Amurka da China ke ganawa a Beijing.
🎧@5:11 Cece-kuce ya ɓarke a jihar Sokoto, Najeriya bayan da gwamnatin jihar ta ware maƙudan kuɗi kusan naira biliyan ɗaya da rabi domin siyan motocin alfarma ga mataimakin gwamna.
🎧@5:20 Gwamnatin jihar Filato ta kafa wani kwamiti na musamman da zai nazarci hanyoyin magance matsalolin tashe-tashen hankula da ke addabar jihar.
🎧@5:30 Za a ji dalilin da ya sa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da gwajin ƙwaya kafin shiga makarantun sakandare a faɗin ƙasar.
🎧@5:51 Shugaba Trump na Amurka ya ce China za ta taimaka wajen buɗe mashigar Hormuz.
🎧@5:56 Firayim Minista na Indiya na neman haɗin kan ƙasashen Gulf da Turai domin sassauta ƙarancin makamashi da duniya ke fuskanta.
🎧@6:04 Gwamnatin Yemen da ‘yan tawayen Houthi sun cimma yarjejeniyar sakin fursunoni fiye da dubu ɗaya da ɗari shida.
DWHausa Rana
Mai gabatarwa: Binta Aliyu Zurmi
🎧@6:40 A Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ‘yan jam’iyyarsa ta APC da su yi ƙoƙarin samun daidaito da haɗin kai yayin da suke gab da fara zaɓen fidda gwani.
🎧@6:53 Albarkacin Ranar Iyali da ake bikinta a yau, za a leƙa jihar Kaduna domin jin yadda matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ke sauya tsarin zaman iyali a arewacin Najeriya.
🎧@7:05 Iran, wadda ke fatan China ta matsa wa Amurka lamba domin cimma yarjejeniyar sulhu da ita, ta sanar da buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwa na China.
🎧@7:32 Jamus ta buƙaci Iran da ta gaggauta buɗe mashigar Hormuz.
🎧@7:37 Iran ta karɓi wasiƙar tayin ci gaba da tattaunawa da Amurka daga fadar White House.
🎧@7:42 Gwamnatin Chadi ta musanta kashe fararen hula a yankin Tafkin Chadi.
DWHausa Yamma
Mai gabatarwa: Binta Aliyu Zurmi
🎧@8:12 Shugaban Amurka Donald Trump ya kammala ziyarar da ya kai China. Za a ji abin da suka tattauna da Xi Jinping.
🎧@8:27 A Najeriya, da safiyar wannan Juma’a ne mayaƙan Boko Haram suka kai hari wata makaranta a wani yanki da ke maƙwabtaka da Chibok a jihar Borno, inda suka kwashe gwamman ɗalibai suka yi cikin daji da su.
🎧@8:41 A Jamhuriyar Nijar, kotun ɗaukaka ƙara a birnin Yamai ta yi watsi da batun ba da beli ga Moussa Tchangari.
🎧@9:03 ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai da dama a jihar Borno, Najeriya.
🎧@9:09 Gwamnatin Libreville na ci gaba da tsare tsohon Firayim Minista na Gabon.
🎧@9:13 Ƙasashe kimanin arba’in sun rattaba hannu kan amincewa da kafa kotu ta musamman kan yaƙin Ukraine.
RFIHausa Hantsi
Mai gabatarwa: Ahmad Abba
🎧@9:45 A Najeriya, ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta gwamnatin ƙasar ta bi sahun takwarorinta na ƙasa da ƙasa irin su Amnesty International, waɗanda suka buƙaci ƙarin haske kan zargin hare-haren sojin sama sun kashe fararen hula.
🎧@10:10 Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya buƙaci ƙasashen Afirka su zama tsintsiya madaurinki ɗaya wajen cin moriyar ɗumbin arzikin da Allah ya albarkaci nahiyar da shi.
🎧@10:16 Shugaban Amurka Donald Trump ya ce China ta amince ta taimaka wajen buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.
RFIHausa Yamma
Mai gabatarwa: Shamsiya Haruna
🎧@10:51 Gwamnatin Chadi ta musanta zargin cewa dakarunta sun kashe fararen hula yayin farmakin da suka kai wa mayaƙan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
🎧@11:04 Hukumar Lafiya ta Afirka ta tabbatar da mutuwar mutum sittin da biyar sakamakon cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
🎧@11:13 Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya ƙulla yarjejeniyar cinikayya ta ban mamaki da takwaransa na China, Xi Jinping.
CRIHausa Yamma
Mai gabatarwa: Abdulrazaq Yahou Zaire
🎧@11:49 Shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping, ya yi wata ganawa ta musamman da shugaban Amurka Donald Trump a ofishinsa na Zhongnanhai.
🎧@11:58 Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta yi bayani kan ziyarar shugaban ƙasar Amurka Donald Trump a ƙasar Sin.
🎧@12:03 Wakilin musamman na shugaba Xi Jinping ya halarci bikin rantsar da shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni.
This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com