Wannan kashin ya yi nazari kan matsayin mace da irin rawar da mata ke takawa da kuma gudunmawarsu cikin al'umma. Shirin ya tattauna da Hajiya Khadija Sa'ad, shugabar kungiyar Babbar Mace da ke jihar Kaduna a Najeriya, kana Zinatu Musa ta baiyana mana irin rawar da take takawa a matsayinta ta uwa.