Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

By DW.COM | Deutsche WelleEducation
Download on the App Store

Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle episodes

  • Kashi na 06 – Ta yaya Sarki Ludwig ya mutu?
    A can fadar Neuschwanstein, Paula da Philipp sun hadu da wata bakuwar fuska sanye da alkyabbar Sarki Ludwig. Sai suka yi wani dan bincike game da sanadin mutuwar Sarki Ludwig.
    Wannan mutumin da ke sanye da alkyabbar Sarki Ludwig ta alfarma, na son su Paula da Philipp su dauka cewa shi ne ainihin sarkin. Ta yaya Ludwig ya mutu? Sai 'yan jaridar suka shirya wani wasa na rediyo don su haska wa masu saurare zargin mutuwar da Sarki Ludwig ya yi a tafkin Starnberg. Ba wanda zai iya tabbatarwa cewa kashe shi aka yi ko kuma shi ya kashe kansa.
    Wannan ganawa da suka yi da wannan shu'umin mutumin wata dama ce ta jin bambance-bambance wajen magana tsakanin 'yan gida da kuma baki. Ku saurari yadda ake fadar taken ban-girma na "Sie" da na wanda ka saba da shi na "du." Lura da tushen kalmar aikatau "sein".
    15 min
  • Kashi na 05 – Sarki Ludwig yana da rai
    Paula da Ayhan sun yi wa sabon abokin aikinsu maraba da shiga Radio D. Da ma suna da wani aiki na gaggawa: Ana rade-radin marigayi Sarki Ludwig na Bavaria yana da rai, don haka suna son su bincika.
    Pilipp ya hadu da sababbin abokan aikinsa, da Paula da Ayhan, ya kuma hadu da miskilar maikula ofis dinsu, Josefine. Lokaci ya kure musu, tun da tuni Philipp da Ayhan sun samo aikinsu na farko. Ana rade-radin cewa shahararren Sarkin nan na Bavaria, Sarki Ludwig II, na nan da ransa, duk da zaton da ake masa ya mutu, ta wani yanayi mai ban mamaki a 1886. 'Yan jaridar sun tafi Fadar Neuschwanstein don su bincika labarin, su kuma gane wa idonsu.
    15 min
  • Kashi na 04 – Jiran sabon abokin aiki
    Jami'an Radio D suna ta jiran Philipp. Wadanda zai yi aiki da su, Paula da Ayhan, suna zaman jira. Sai dai ba Philipp ba alamarsa, ga shi waya ba ta shiga.
    A sakamakon rashin kyan yanayi, sai da Philipp ya makara. Ya yi kokarin kiran Paula ta waya don ta san halin da yake ciki, amma bai same ta ba. A karshe, sai Paula da Ayhan suka bar ofis. Wayar da mahaifiyar Philipp ta bugo sai ta dada rikita al'amura.
    Philipp ya nemi afuwar makarar da ya yi. A wannan kashi, za ku ji hanyoyin neman afuwa dabam-dabam.
    15 min
  • Kashi na 03 – Tafiya Berlin
    Ga Philipp can ya nufi Berlin. Sai dai saboda rashin kyawun yanayi, tafiyar ba ta sauri. Har abokai Philipp ya yi a hanya.
    Philipp dai ya tafi filin jirgin sama na Munich a mota, inda ya yi niyyar shiga jirgin sama zuwa birnin Berlin. A saboda ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya, sai tafiyar tasa ta tsawaita.
    A wannan kashin, za mu ji yadda ma'aikacin shirin Radio D, wato Philipp da mahaifiyarsa, za su gabatar da kansu kamar yadda ya kamata. Za ku ji yadda ake gabatarwar tsakanin 'yan gida da baki.
    13 min
  • Kashi na 02 – Waya daga Radio D
    Philipp har yanzu bai samu hutun da yake so ba. Bayan gama fafatawa da kwaron da ya dame shi, sai ya fuskanci hayaniyar makwabta. Yayin da kwatsam aka yi masa waya daga Berlin, sai ya baro kauyen a gaggauce.
    Bayan fafatawar da Philipp ya yi da kwari a can, sai ga karar zarto, da hayaniyar wani da yake koyon busa. Duk abubuwa dai sun taru sun dame shi. Don haka, yayin da Paula ta Radio D ta kira shi daga Berlin, sai Philipp ya sami dalilin katse ziyararsa ta kauye. Philipp dai ya yi ban-kwana da mahaifiyarsa wadda ba ta ji dadin tafiyarsa ba, daga nan sai ya garzaya babban birnin kasar Jamus.
    Idan ma Jamusancinku bai nuna ba, za ku iya fahimtar abin da yake faruwa a wannan kashin. Kalmomin da ake amfani da su na yau da kullum, da kuma karin muryar da ake amfani da shi, za su taimaka muku wajen fahimtar shirin da kuma iya saurarensa.
    12 min
  • Kashi na 01 – Ziyara zuwa kauye
    Philipp wani matashi ne, ga shi can yana tuka mota zai ziyarci mahaifiyarsa mai suna Hanne a kauye. Ya yi shirin shakatawa a can, amma kuma sai ya tarar da yanayin zaman kauye na da irin nasa matsalolin.
    "Kauye da dadi yake!" in ji Philipp, a yayin da ya isa kauyen da mahaifiyarsa take, inda kuma yake son ya huta daga hayaniyar birni. Sai dai ba shanu da maguna kawai ya tarar ba, har ma da wasu halittun. Yana cikin shan kofi a lambu, sai wani kwaro ya bata masa lissafi. Daga nan sai abubuwa suka fara dagule wa Philipp.
    Ko masu sauraro ba su iya Jamusanci sosai ba a yanzu, za su iya fahimtar abin da ke kunshe a wannan kashin. Don kuwa hayaniyar da ake ji a bayan fage, ta isa ta bayyana inda Philipp yake. A wannan kashin, za ku koyi yadda ake yin gaisuwa da ban-kwana.
    15 min

About Shirin Radio D zango na 1 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

From the publisher's feed

"Radio D" yana magana ne akan wasu wakilan jarida guda biyu tare da al'amuransu masu kayatarwa. Wannan kwas na masu koyo a matakin farko yana da manufa kan auna fahimtarsaurare. Akwai takardu da…