Tafsirin Surah Âl-`Imrân:
Darasi Na 116
[Surah Āli-ʿImrān: 164]
{ لَقَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِینَ إِذۡ بَعَثَ فِیهِمۡ رَسُولࣰا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ یَتۡلُوا۟ عَلَیۡهِمۡ ءَایَـٰتِهِۦ وَیُزَكِّیهِمۡ وَیُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَـٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُوا۟ مِن قَبۡلُ لَفِی ضَلَـٰلࣲ مُّبِینٍ }
*Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo OON (Hafizahullah)*
23-2-1448
07-08-2026
1. Daga cikin dalilan da suka sa Allah ya aiko Annabi (S.A.W) daga cikin Larabawa.
- kasancewar su masu dangantuwa da Annabi Ibrahim (A.S)
- Rashin tasirantuwar su da manyan addinai na wannan zaman in
- kasancewar su al'ummar da ba a taba yi musu mulkin mallaka ba.
- kasantuwar su al'ummar da ba su wani ilimi rubutacce a tare da su.
- kasancewar su a tsakiyar duniya a wancan lokacin.
- kasantuwar su al'umma mai shaja'a marar tsoro.
- kasancewar su suna rikar abu da gaske ba sa yi wa rikon laga-laga.
- kasancewar su mutane ne masu fadar gaskiya a duk inda suke.
- kasantuwar su mutane masu hankali kuma masu hikima.
- kasancewar su mutane masu kaifin da karfin kwakwalwa.