*Fatawoyin Rahma*
Lahadi 7/12/1447 - 24/5/2026
Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
Shimfida: _Kashe- Kashe Da Ke Faruwa A Cikin Al’uma_
Tambayoyi da Amsoshi:
1. Hukuncin Zoben Ƙarfe!
2. Hukuncin zuwa kallon ƙwallon ƙafa ga mata.
3. Akwai iyakar shekaru ga Mata da za su je Sallar Juma’a?
4. Hukuncin tsefe gashi ga mace mai al’ada?
5. Hukuncin rance da ‘cooperative’ ta ke bawa ma’aikata!
6. Wanda yayi bakance zai iya azumi ,ya fara azumin amma saboda wahala zai iya ciyarwa maimakon azumin?
7. Hukuncin auren da iyaye suka wakilta wani ya karɓawa ɗansu (angon) auren ?
8. Menene hukuncin auren da miji ya cewa matarsa ‘auren mu da ke ya zo ƙarshe’?
9. Hukuncin wanda yayi salloli da janaba?
10. Hukuncin ware ranar Juma’a da azumi?
11. Yaya ake kin yin tasbihin bayan Sallah?
12. Ana iya yin Salati ga Annabi ﷺ yayin khutbar Jumu’a?
13. Uwa za ta iya hana ɗanta gado?
14. Ya hallata a yi taimama akan ‘Tiles’?
15. Menene hukuncin zubar da ciki saboda tsoron talauci?
16. Hukuncin cin naman Maciji?
17. Wanda aka ba shi bashi zai iya biyan bashi da kaurarawa?
18. Mutumin da ya aikata wasu laifuka sannan ya tuba; dole sai ya bayyana abubuwan da yayi a baya?
19. Menene hukuncin bashi da ruwa saboda buƙata?
20. Ya hallata ayi amfani da DNA don jinginawa mutum ɗa?
21. Yaya hukuncin musulma da ta auri kafiri?
22. Hukuncin mummunan zancen zuci ga mai son yi ibada!
23. Wacce addu’a mutum zai yi yayin sa gawa a ƙabari!
24. Mutum zai iya yin addu’ar buɗe Sallah da Hausa?