
Sign up to save your podcasts
Or


Dr. Mansur Sokoto ya bamu lokaci don tattaunawa kan matsalar shaye-shaye. Wallah Shaye-Shaye babbar matsala ce da mutanne ke daukan ta qarama. Lokacin da mukayi nazarin illoli da ci baya da wannan mugunyar dabi'a ke tattare da ita, to fa nan take zamu fahihimci cewa ta wuce duk tunanin mu. A wannan tattaunawar, Dr. ya bayyana mana menene kayan maye, yadda ake gane dan shaye-shaye da hanyoyin rigakafi da magance wannan matsalar shaye-shaye.
Ku ba mu mintoci kadan don sanin "Mahangar Mu"
Yau matasa da dama sun kamma karatu amma ba abin yi.
Shin wai manene matsalar ne?
Wai ina aka kuskure sannan ina mafita?
Saurari wannan maqala don jin Mahangar Mu.
Ga wata matsala da aka sanya shububa akan ta.
Idan kana son ganin cikakken tsari da ta shafi duk wani fanni na rayuwa, babu shakka ka dubi tsari da Annabi ya dora Sahabbai akai. Duk wata kafa wadda idan an bi ta, za a samu natija, to fa sai da ya karantar da su. Wurin da yake aibi ne kuma, ya nuna ma su, sannan ya shiryar da su tafarki wanda zasu iya gano abin da ya ke dai-dai, da kuma akasin haka.
Ta wannan hanyoyin suka bi suka gano har da abin da bai fito qarara ya nuna ma su hukuncin sa ba.
To kan wannan matsala, shin "Murna Zanyi Ko Hisabin Kai?
Wannan podcast, mun tattauna kan matsaloli biyu, A yi qoqari a saurara har karshe.
Sau da yawa mutane na fadawa cikin halaka saboda wani shawara da suke samu daga wasu. Aure da yawa sun mutu, jari da yawa sun karye, zumunta da yawa sun yanke duk saboda shawara da a ka basu. Mu kame bakin mu idan mun san cewa ba mu da shawarar da za mu bayar. ba dole sai mun yi magana ba idan bamu da masaniyar al'amura.
Wai aka ce "Zo mu zauna, zo mu saba".
Shin wannan matsalar wani shawara ne a Mahangar ka, kake gani zata yi aiki don sasanta sabanin maaurata tunda dai rayuwa ta tabbatar mana inganci wannan magar da muka kawo.
Mu dai, idan ka saurari wannan shiri, za ka fahimci Mahangar Mu.
Kun taba la'akari da yadda muke gudanar da bukukuwan mu yau kuwa?
Menene laifi ko kurakurai da muke yi a hidimar bikin mu?
Wasu abubuwa ne laifi ba da muke yi?
Shin menene haduran laifukan da muke yi a rayuwar aure bayan buki?
Yaya zanyi in gyara matsalar da na riga na jefa kaina a ciki?
Ku saurari Mahangar Mu don samun amsoshin wadannan tambayoyi.