Shirin ya duba gasar karatun alkurani da aka shirya a jihar Yobe domin zabo gwarzaye da za su wakilci Najeriya a gasar duniya da ake yi, inda aka samu manyan baki da Sarkin Musulmin Najeriya.
Shirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
Shirin ya duba muhimmancin tagwaye a lokacin aure a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar, inda ake gayyatar 'yan biyu da ke a cikin gari da kewaye domin kawo gudurmuwa a wajen bikin 'yan biyu.
10 min
About Taba Ka Lashe
From the publisher's feed
Shirin al´adu, addinai da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi dabam-dabam a duniya. Taba Ka Lashe shiri ne da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummomi da mabiya…
addinai dabam-dabam a duniya da zummar kyautata zamantakewarsu, zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakani. Muna gabatar muku da shirin ta rediyo a kowane mako, kuna kuma iya sauraronsa a shafinmu na Internet da kuma ta kafar Podcast.