Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Zama Da Uwar Miji A Gida Daya: Inda Gizo Ke Saka

    Rigingimu tsakanin ma'aurata dake samo asali daga zama wuri daya da iyayen miji musamman uwa na daya daga cikin matsalolin da ake fama da su a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya. 

    Tarihi ya nuna, an yi zamanin da iyaye da 'ya'ya ke zama wuri guda lafiya, mene ne ya canza da a wannan zamanin ba a iya zama wuri guda da iyaye kuma a zauna lafiya? 

    Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadanda abin ya shafa, ya ji ta iyayen, ya ji ta 'ya'yan, ya kuma nemi shawarwarin masana kan mafita. 

    31 min
  • Yadda Iyaye Ke Kashe Wa 'Ya'yansu Aure A Arewa

    Mutuwar aure daya ce daga cikin matsalolin da ke ci wa mutanen Najeriya musamman 'yan Arewacin kasar tuwo a kwarya. 

    Ko kun san wadansu iyayen ne da kansu suke janyo mutuwar auren 'ya'yansu? 

    Shirin Daga laraba na tafe da karin bayani, ciki harda wanda aka kashewa aure. 
    A yi sauraro lafiya. 

    30 min
  • Amfanin Kishiya A Zamantakewar Aure

    Musulunci ya halatta auren mace fiye da daya ga mazan da ke da hali kuma wadanda za su iya yin adalci, amma kuma a rayuwarmu ta yau babu abin da ke ganin adawa da shan kushe kamar karin aure,

    Shin mene ne amfani kishiya?

    Wannan karo shirin Daga Laraba ya yi kokarin gano  muhimmancin kishiya da kuma amfaninta. 



    30 min
  • Yadda Mutane Ke Zubar Da Ladan Azuminsu Kafin Sallah

    Malamai na karfafa wa mabiya addinin Islama guiwa a watan Azumin Ramadana wurin  tsayuwar  daka wurin Ibada, amma wani abin mamaki shine yadda a karshen watan azumin mutane ke  shagalta har su kai ga haramun wurin  bikin Sallah.

    Shin kun san labarin masu tara kudi domin shirya bikin tarbar shaidan? 

    Shirin Daga Laraba na wannan karon ya dubi hanyoyin da maza da mata ke bi wurin zubar da ladan ayyukan da su ka yi a cikin watan Azumin Ramadana. 

    31 min
  • Yadda Rashin Ruwan Sha Ke Lakume Rayuka A Kano

    Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da suka ci gaba a fannoni da yawa na rayuwa. Sai dai wani bincike da muka gudanar ya bankado yadda ake shan wahalar ruwa a wasu yankunan wannan jiha. 

    Mene ne ya sa har yanzu ake tsananin wahalar ruwa a Jihar Kano? 

    A saurari shirin DAGA LARABA na wannan mako a ji yadda ya bankado bakar wahalar da mutane ke sha  sakamakon rashin ruwa a wasu yankunan Jihar Kano. 

    27 min
  • Hukuncin Saka Hotunan Sadaka A Soshiyal Midiya

    A watan azumin Ramadan an kwadaitar da Musulmai falalar yawaita sadaka da kyauta domin neman yardar Allah.

    Shin mene ne hukuncin masu daukar hotunan sadaka da kyautar da suka bayar su saka a kafafen sada zumunta na zamani wato oshiyal midiya?

    Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da bayanan hujjojin masu saka wadannan hotuna da kuma matsayin Malaman addinin Musulunci a kan wannan dabi’a.

    30 min
  • Dalilin Da 'Yan Siyasa Ke Kin Karbar Kaye A Najeriya

    A tsarin zabe dole a samu wanda ya ci, a kuma samu wanda ya fadi. Amma wannan ka'ida har yanzu ba ta samu wurin zama a fagen siyasar Najeriya ba, don kuwa duk wanda ya fadi baya yarda ya fadi sai ka ji suna kiran "Magudi aka yi, amma ni na ci zabe".

    Mene ne dalilin da 'yan siyasar Najeriya ke  kin karbar kaddarar faduwa?

    Saurari shirin Daga Laraba domin jin dalilin 'yan siyasa na kirkirar wannan dabi'a  ta kin karbar kaye a matsayin kaddara da ke shafawa Najeriya bakin fenti a idanun duniya. 

    30 min
  • Matakan Samun Nasara A Watan Ramadan

    Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda. 

    Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata? 

    Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan. 

    31 min
  • Hakikanin Abin Da Ya Sa Aka Ki Sakin Naira

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa.

    Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira?

    Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka.

    Za ku so karanta wadannan

    30 min
  • Wane Ne Bola Ahmed Tinubu? Bayani Daga Dattawan Legas

    Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa.

    Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari?

    Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu.



    30 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…