Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Yadda Ake Aure Da Ciki A Kasar Hausa

    Shin idan ka gano cewa da cikin wani amaryarka ta shigo gidanka wane mataki za ka dauka?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya bankado al’ada yin aure da juna biyu a Arewacin Najeriya.

    Shin da sanin angwaye ake daura musu aure da mata masu ciki?

    Gyara zama domin jin yadda ta kaya tsakanin wadansu angwaye da amarensu suka zo musu da cikin wasu.

    30 min
  • Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa

    Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya.

    Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba?

    Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya.



    31 min
  • Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne?

    Shin me ya sa kayayyaki marasa inganci suka zama ruwan dare a Najeriya?

    Wani lokacin kayayyaki na jabu ko lalatattu da ake sarrafawa ko sayar wa ’yan Najeriya na hallaka da dama a cikinsu.

    Me hukumar da ke kula da ingancin kayayyaki ke yi don hana kawo wa ’yan Najeriya kayayyaki marasa inganci?

    Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin wainar da ake toyawa.

    31 min
  • Yadda Zubar Da Ciki Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya

    Zubar da ciki al'amari ne mai ba da tsoro saboda hadarinsa da kuma alhakin da ake iya dauka idan an yi ba bisa ka’ida ba.

    Shin ko mene ne dalilin da zubar da ciki ya zama ruwan dare a tsakani ’yan mata da matan aure a Najeriya? 

    Saurari cikakken shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin yadda matan aure da ’yan mata suka maida zubar da ciki abin wasa.

    30 min
  • Maganin Karfin Maza: Gyara Ko Janyo Ciwo?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya mayar da hankali ne a kan maganin karfin maza, amfaninsa, illolinsa da kuma shawarwarin masana a kai.

    Wannan kari ne a kan shiri na musamman da muka kawo muku a baya kan maganin mata, wanad aka fi sani da kayan mata da yadda ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman a Arewacin Najeriya.

    30 min
  • Yadda Yi Wa Kananan Yara Fyade Ya Yadu A Arewacin Najeriya

    Me ya sa ake yawan samun mutane masu manyan shekaru da ke afka wa kananan yara mata ko mazayarinya ko karamin yaro?

    Shin wane dalili ke sa kawo yawaitar wannan kazamar dabi’a ta lalata da kananan yara?

    Shirin Daga Laraba ya dubi yadda wannan matsala ta zama ruwan dare, musamman a Arewacin Najeriya.

    A yi sauraro lafiya.



    31 min
  • Abin da kishi ke sa maza aikatawa

    Duk lokacin da aka ambaci zafin kishi, to da dama mata ke zuwa zukatan jama’a.

    Shin yaya maza ke kishi, kuma me suke iya aikatawa saboda tsananin kishi?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da tsananin kishin maza, abin da yake iya sa su da kuma yadda ya kamata a yi kishin.



    30 min
  • Yadda Masu Aure Suka Zama Mazinata A Najeriya

    Ana samun korafe-korafe game da yaduwar zinace-zinace tsakanin ma’aurata a Najeriya? 

    Shin me ya faru ma’aurata suka tsunduma ka’in-da-na’in a harkar alfashar da a baya an fi dangantawa da marasa aure marasa kamun kai?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tsananta bincike da  tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan wannan batu domin gano inda gizo ke saka, domin fid-da jaki daga duma.



    31 min
  • Yadda Aka Zalunce Mu A Bainar Jama’a, Amma Kowa Ya Kau Da Kai

    Taimakon juna na daya daga cikin hallayyar da ake kwatanta mutane masu nagarta da shi, amma a yanzu abin yana neman zama tarihi.

    Shin me ya sa taimakon juna ya yi karanci a wannan zamanin?

    Saurari labarin wadansu da aka zalunta a gaban jama’a amma ba a kawo musu dauki ba.

    Mun kuma tattauna da masana kan yadda aka tsinci kai a halin rayuwar ba ruwan kowa da kowa.

    30 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…