Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • ‘Ina Sayar Da Kwalaba 1,000 Na ‘Kurkura’ A Mako A Zariya’

    Shin da gaske ne ‘Kurkura’ na maganin basir, ko dai shigo-shigo ba zurfi ake yi wa jama’a su fara shaye-shaye?

    Kurkura wani magani mai guba da kuma sa maye nan take idan an zuba shi a baki.

    Sai dai kuma duk da haka, yana ci gaba da samun kasuwa a tsakanin jama’a musamman a Arewacin Najeriya da sunan maganin basir da karin kuzari.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi wa wannan batu duba na musamman ta hanyar tattaunawa da masu sayarwa, masu sha da kuma likitoci.

    31 min
  • Daga Lahadin Nan INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zaɓe

    Hukumar Zabe ta kasa, INEC; za ta rufe Yin rajistar katin Zabe ranar Lahadin nan Mai zuwa, wato 31 ga watan nan na Yuli.

    Idan za a iya tunawa hukumar Zaben ta kara wa'adin yin rajistar katin Zabe na wajen wata daya.

    Amma duk da haka, jama'a da dama na korafe -korafen cewa lokacin bai ishe su ba, tunda har yanzu akwai mutane adadun da ba su yi rajistar ba.

    Mun tattauna da 'yan Najeriya, da hukumar ta INEC.

    31 min
  • Dalilan Da Daliban Kano Ke Yawan Faduwa Jarabawa

    Ko me ya sa harkar ilimi, musammam a Arewacin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi, har yana neman mutuwa?

    A makonnin baya, mun kawo muku yadda harkokin ilimi ke tafiya a jihohin Bauchi, Kebbi, Sakkwato da Zamfara.

    Yau ga mu a Jihar Kano, inda muka yi tankade da rairaya kan yadda dalibai ke yawan faduwa jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma JAMB, wadda ake zanawa domin sharar fagen shiga jami’a.

    Mun tattauna da dalibai da kuma masu ruwa da tsaki a kan wannan lamari.

    31 min
  • Matsalar Tsaro Da Rashin Tsari Ne Suka Kara Ruguza Ilimi a Zamfara

    Idan ana biye da mu, a cikin shirin Daga Laraba na makon jiya, mun tattauna ne a kan harkar ilimin jihar Sakkwato, a wannan makon kuma, mun tabo harkar ilimin jihar Zamfara ne.

    Ilimi aka ce shi ne gishirin zaman duniya, amma idan ba ilimi, sai jahilci ya yi katutu.

    Masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin jihar Zamfara, sun alankanta rashin tsaro a matsayin matsala ta farko kuma babba da ke ci wa ilimi a jihar tuwo a kwarya.

    Shirin Daga Laraba ya leka Jihar Zamfaran inda ya tattauna ya kuma jiyo dalilan tabarbarewar ilimin jihar.

    30 min
  • Halin Da Harkar Ilimi Ke Ciki A Jihar Sakkwato

    Idan ba ku manta ba, makonni biyu da suka gabata, mun tattauna ne a kan tsarin ilimin Jihar Bauchi da na Jihar Kebbi.
    A wannan makon kuma mun karkata ne zuwa kan tsarin ilimin Jihar Sawkwato.

    A yayin da ilimin daliban firamare da sakandare ke tabarbarewa, iyaye da malamai na kokawa kan irin kalubalen da baganren ilimin jihar ke fuskanta.

    Laifin waye kuma ina mafita? Shirin Daga Laraba ya tattauna da masu ruwa da tsaki.

    31 min
  • Ainihin Halin Da Harkar Ilimi Ke Ciki A Jihar Kebbi

    Batun lalacewar harkar ilimi a Jihar Kebbi ba sabon labari bane a kunnuwan 'yan Najeriya, musamman batun daliban da ke jarrabawar sharar fagen shiga jami'a.

    An jima ana kwarmata batun lalacewar gine-gine da rashin kwararrun malamai da kayan koyarwa a jihar, domin samar da ilimi mai inganci.

    A wannan karon, shirin Daga laraba ya yada zango a bangaren ilimin Jihar Kebbi domin bankado irin badakalar da bangaren ke ciki da niyyar neman mafita. 

    30 min
  • Halin Da Karatun Boko Ke Ciki A Jihar Bauchi

    Rahotanni kan halinda makarantu da karatun boko ke ciki a Jihar Bauchi na cigaba da janyo takaddama a tsakanin jama'a. Biyo bayan sabbin tsare-tasren da gwamnatin jihar ta kawo.

    Wadanne tsare-tsare ne wadannan da jama'a ke tattaunawa akansu, kuma ta wadanne hanyoyi suka shafi rayuwar jama'a.

    Shirin Daga Laraba na wanna mako ya yada zango a Jihar Bauchi domin binciko gaskiyar abinda ke faruwa.

    30 min
  • Yadda Cin Zarafi Da Bidiyon Tsiraici Ke Zama Ruwan Dare

    A yan shekarunnan amfani da bidiyon tsiraici domin cinma burika ke neman zama ruwan dare a cikin jama'a.

    Mene ne akayi ba dai-dai ba har wannan dabi'a ta samu karbuwa  a tsakanin matasa da wadansu manyan?

    Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin gano bakin zaren. 

    30 min
  • Alakar Matar Gida Da Dangin Miji

    Sau da dama ana samun rashin jituwa tsakanin dangin miji da matar dan uwansu, a wadansu lokutan ma har ya kai ga ya shafi 'ya'yansu. 

    Daga ina matsalar take, sannan me ake yi ba daidai ba? 

    Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin neman mafarin wannan fitina da kuma hanyoyin da za a bi domin warware ta. 

    30 min
  • Jikoki A Hannun Kakanni Tausayi Ko Cutarwa?

    Mutane da dama na tura 'ya'yansu wurin kakanninsu da sunan ziyara ko su zauna su rayu dasu da sunan taimakon kakannin. 

    Anya taimako ne kuwa?

    lura da yadda rainon mutum yake da wahala, kaiwa mutum mai shekaru raino ba janyo sabuwar wahala  bane? 

    Shirin namu na yau ya mayar da hankali akan wannan dabi'a. mun tattauna da wadansu kakanni da kuma malaman addini domin sanin gaskiyar abinda ya sa ake hakan. Sun kuma bada shawara domin inganta zamantakewa.  

    30 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…