Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Yadda ’Yan IPOB Suka Kashe Mai Tsohon Cikin Da ’Ya’yanta

    A cigaba da ayyukan 'yan ta'addan IPOB a Kudu maso Kudancin Najeriya, yan kungiyar sun kai farmaki yankunan da Hausawa ke zaune inda suka hallaka wata mata mai dauke da cikin wata tara da 'ya'yan ta hudu a Isolo dake Jihar Anambra.

    Bayan nan rahotanni da muka samu sun nuna cewa a kasa da awa 24 bayan kashe matar nan da 'ya'yanta, yan haramtacciyar kungiyar sun sake kashe wasu yan acaba 4 sun kuma kone gawar daya daga cikin su, sannan kuma sun kashe wani mahauci. 

    Ko wane hali 'yan Arewa mazauna yanki ke ciki a yanzu?

    Muna tafe da bayanan yadda aka kashe mata mai cikin nan da kuma karin bayani kan halin da 'yan Arewa mazauna yankin ke ciki a halin yanzu.

    31 min
  • Yadda Za A Magance Matsalolin Matasan Arewa

    A makon da ya gabata mun binciko matsalolin matasan Arewa da kuma dalilan da aka bar su a baya.

    A shirinmu na wannan karon mun tattauna da wadansu matasan yankin, wadanda da suka san matsalolinsu da kuma maganin matsalolin.
    Matasan sun bayyana ainihin abin da ke hana su ci gaba, sun kuma bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a shawo kan matsalolin nasu.

    30 min
  • Dalilin Da Muka Bar Matasan Arewa A Baya

    Yara manyan gobe, inji Hausawa; amma anya matasan Arewacin Najeriya sun samu damar zama manyan goben yadda ya kamata?

    In aka yi la'akari da halin da matasan Arewan ke ciki, wani abin tambaya shi ne, ko dai su a yarintar za su kare?

    Me ke kawo musu wannan tarnaki?

    Shirin Daga Laraba ya tattaro fahimtar masana da matasa kan ababen da ke mayar da  matasan Arewa koma baya.

    31 min
  • Anya Akwai Ranar Da Za A Wayi Gari Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Zama Tarihi A Najeriya?

    Ta'addancin 'yan bindiga ya zamo ruwan dare a Najeriya. Domin babu nau'in da ba a gwada irinsa a kasar nan ba. 

    Anya akwai ranar da wannan ta'addanci zai zamo tarihi kuwa?

    Mene ne ya kamata ayi domin a gaggauta kawo karshen ta'addanci, wane ne ya kamata a sa a gaba domin neman mafita, mene ne ake yi daidai kuma mene  ne ake bukatar a gyara?

    Mazauna yankunan da 'yan ta'adda ke ciwa tuwo a kwarya sun yi mana bayanan halin da suke ciki da kuma tunaninsu dangane da yiwuwar kawo karshen ta'addanci. 
    Mun kuma ji ta bakin masana harkokin tsaro domin sanin nasu hasashen kan karshen ta'addanci a Najeriya. 

    30 min
  • Yadda Za A Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya —Masana

    Rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na nema ya gagari kundila. 

    Mene ne ake yi ba daidai ba, wa ya kamata ya amsa tambayoyin da jama'a ke yi kan yadda za a warware matsalolin tsaron?

    Masana sun yi wa Shirin Daga Laraba na wannan makon bayani kan hanyoyin da suka dace a bi domin warware matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa.

    30 min
  • Kokarin Da Gwamnati Ke Yi A Yakar ’Yan Ta'adda

    Yawan hare-haren da ’yan ta’adda ke kaiwa kan jama'ar da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Neja da Kaduna, ya sa shakku a zukatan ’yan Najeriya bisa kokarin da Gwamnati ke cewa tana yi.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya binciko irin kokarin da gwamnatin ke yi a matakin kasa da jihohin da abin ya fi shafa.

    30 min
  • Abin Da Muka Gani A Dabar ’Yan Ta’adda

    Satar mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya.

    A wane hali mutanen da ake sacewa ke tsintar kansu a hannun masu garkuda da mutane da kuma bayan an sako su?

    Shin yaya wadanda ke satar mutane ke tunani?

    31 min
  • Barnar Da 'Yan Bindiga Suka Yi A Arewa Maso Yammacin Najeriya

    A makon da ya gabata, cikin shirin Daga Laraba mun kawo muku bayanin asalin ta'addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda kuka ji yadda abubuwa suka faro daga Jihar Zamfara

    A wannan karon, shirin ya bankado irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi da kuma yadda zamantakewa ta lalace tsakanin jama'ar wannan yanki a sanadiyyar ta’addancin ‘yan bindiga.

    31 min
  • Asalin ta’addanci a Zamfara

    Jihar Zamfara ta yi suna a duniya a shekarar 2000, sanadiyyar  kaddamar da shari’ar Musulunci.

    Jama’a sunyi ta zancen Jihar da sa albarka, suna kuma kallon ta a matsayin wani wuri da za a samu wanzuwar adalci saboda abinda ake sa ran wannan sabon tsarin mulkin zai tabbatar.
    Sai dai a baya-bayanan, Jihar ta tsinci kanta a bakin jama’a a wannan karon ana tir da abinda ke fitowa na ta’addanci da duk wani irin rashin mutunci da mai tunani zai tunano.

    Daga ina wannan matsala ta samo asali?

    Su wa ake zargi da shuka wannan bala’i da ya addabi yankin Arewa baki daya?

    32 min
  • Ina Makomar Masu Yada Labaran Karya A Lahira?

    Makonni biyar ke nan da shirin Daga Laraba ya fara fede biri har wutsiya kan batun labaran karya domin gano asalinsa da masu amfana da shi da masu yadawa da kuma amfanin da su ke samu.

    Yadda Ake Gane Labaran Karya ne batun da shirin Daga Laraba na makon da ya gabata ya mayar da hankali a kai.

    A wannan makon kuma shirin ya karkata ne kan  Irin Kallon Da Addini Ke Yi Wa Labarin Karya.

    Mun tattauna da malaman addinin Islama da na Kirista domin sanin makomar masu yada shi a wurin ubangiji.



    25 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…