Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Matakan Yin Katin Zabe Domin Kawo Sauyi

    Zabe na yi wu wa ne idan a kwai masu zabe, nan da watanni 13 za’a gudanar da babban zabe a Najeriya.

    Shin kun san yadda zaku yanki katin zabe?
    Idan kun sauya unguwa ko gari wadanne hanyoyi zaku bi wurin karbar sabon katin da zai baku damar zabe a duk inda kuke?

    Shirin Daga Laraba na wannan makon ya tattaro bayanan matsalolin da a ke fuskanta wurin yankar katin zabe, da hanyoyin da za’abi wurin warwaresu a cikin sauki.

    30 min
  • Yadd kuri'arku za ta iya sauya rayuwarku

    Tun da aka dawo mulkin Dimokuradiyya a Najeriya a 1999, yawan masu kada kuri’a sai raguwa yake ta yi, ko mene ne dalili?

    Anya masu zabe sun san irin karfin da kuri’arsu take da shi kuwa?

    Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da amsar wannan tambaya har ma da bayanin amfanin zabe da muhimmancinsa wurin kawo sauyin rayuwa  mai ma’ana.

    A yi sauraro lafiya.

    30 min
  • Karfin Ikon Talakawa A Dimokuradiyyar Gaskiya

     An fara mulkin dimokuradiyya ne a Karni na 17 bayan kafa kasar Amurka, jim kadan bayan juyin juya hali.

    Shi ne tsarin mulkin da ya bai wa ′yan kasa damar fadin yadda suke so a mulke su.

    Hakan ta sa suke da damar tofa albarkacin bakinsu a harkokin gwamnati ta hanyar wakilansu da suka zaba zuwa majalisu a matakai daban-daban.

    Shirin Daga Laraba na wannan karon na kunshe da bayani kan nau’ikan tsarin dimokuradiyya da kuma yadda take tafiya a Najeriya, Afirka da ma sauran kasashen da suke morar tsarin.

    35 min
  • Illolin da rashin kaunar juna ke yi wa mata

    A shirin Daga Larabar da ya gabata, mun yi duba ne a kan Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu.
    A kashi na biyu da za ku saurara a wannan karon kuma, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda rashin kaunar juna a tsakanin mata ke hana musu ci gaba a fannoni da dama na rayuwa.
    A yi sauraro lafiya.

    32 min
  • Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu

    Mata na yawan ambaton kansu da zumunci a tsakaninsu har sukan bugun kirji da cewa ‘ciwon ’ya mace na ’ya mace ne.’

    Amma a zahiri ko takarar siyasa mace ta tsaya, ’yan uwanta mata ke fara yaƙarta kafin maza?

    Me ya sa kishi ya yi yawa a zukatan mata har ba sa iya bari mijinsu ya auro kawarsu su zama abokiyan zama? Ina ciwon ’yan macen?

    Shin ko’ina haka abin yake, ko a Najeriya ne kadai?

    Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya rairayo manyan dalilan da mata ke yawan samun rashin jituwa a tsakaninsu.

    A yi sauraro lafiya.

    31 min
  • Yadda 'Yan Siyasar Kano Ke Hana Jihar Ci Gaba

    Masana sun bayyana yadda ’yan siyasar Kano ke hana Jihar ci gaba, lura da yadda siyasar gaba ta maye gurbin siyasar hamayya da kishin jihar.

    Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi waiwaye kan yadda aka faro siyasar Kano, wuraren da aka wuto, da kuma halin da ake ciki a yau.

    31 min
  • Kunci da wulakancin da zawarawa ke fuskanta

    sanin gaskiyar halin da zawarawa ke ciki sai in ka sauraresu, wai me ya sa ba'a son auren bazawara, wa ya kamata ya dauki nauyin ta, shin zawarci zabin kai ne, ko kuma kaddara ce, ya ya mutane ke kallon bazawara? 
    Saurari irin halin kuncin da mata ke samun kansu da zarar sun rasa auren su. 

    30 min
  • Auren Wuf: Soyayya ko kwadayi?

    Mutane na yiwa auren wuf ko auren caraf fassara daban-daban lura da yadda auren yake.

    wasu na ganin auren wuf a matsayin auren cin kasuwar bukata,  amma a zahiri me yasa akeyin auren wuf, meye alfanun yin shi, yanada illa ko kuwa?

    30 min
  • Illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi

    A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna dabi’ar bilicin, wato jeme launin fatar jiki daga baka ta koma fara.

    A yau za ku ji illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi,  kuma za ku ji yadda wannan dabi’a ta bilicin ta mamaye, daga maza har  mata.



    1 hr 1 min
  • Me ya sa ake bilichin?

    A wannan karon, shirin Daga Laraba ya mayar da hankali ne a kan masu canza wa kan su kama. Masu canza launin fatar jikinsu daga baka ta koma fara. Wato masu Bilichin.

    A kashin farkon shirin, mun duba dalilan da ke sa mutane su na canza kamanninsu da Allah Ya halicce su da shi. 



    33 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…