Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Halin Ni-'Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan 'Yan Gudun Hijira?

    Mummunan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a sansanoni daban-daban a wasu sassan Najeriya ba bakon abu ba ne.

    Abin da kan zama bako shi ne samun wani mawadaci ko kungiyar mawadata su tallafa wa wadannan mutane.

    A wannan shiri na Daga Laraba mun duba abin da ya sa masu hannu da shuni ba su cika taimaka wa wadannan bayin Allah ba.

    31 min
  • Abin da ke kawo yawan sakin aure a kasar Hausa

    Mutuwar aure kullum karuwa take yi a Arewacin Najeriya.

    Mene ne dalili, kuma laifin wane ne? Daga ina matsalar ta samo asali? Mece ce mafita? 

    A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi kokarin nemo amsoshin wadannan tambayoyi da ma fahimtar masana a kan wannan matsala.

    31 min
  • Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ke Rashin Lafiyar Kwakwalwa

    Matsalar rashin lafiyar kwakwalwa da jirkicewar tunani larura ce da kwararrun  likitoci ne kadai ke iya maganinta 

    An dai kiyasta cewa 'yan Najeriya miliyan 20 ne ke fama da wannan larura. 

    A wannan  karon, mun tattauna a kan me ke kawo matsalar, da kuma hanyoyin da za a bi domin kauce mata, da magance ta.

    32 min
  • Tsadar kayan abinci: 'Yan Najeriya na dandana kudarsu

    A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya baje tsananin tsadar kayan abinci a faifai don gano abin da ya haddasa ta, wane ne ya haddasa ta, dalilin haddasa ta, da hanyoyin magance ta.

    'Yan kasuwa da masana da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana dalilan tsadar, sun kuma  bayar da  shawarwari a kan yadda za a rage radadin da talaka ke fama da shi.



    31 min
  • Yadda Hadurra ke lakume Rayukan Dubban 'yan Najeriya


    Wasu alkaluma da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) ta fitar sun nuna cewa a wata guda kawai mutane 1,059 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hadurran mota a Najeriya.

    A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yawan hadurra da dalilan da ke haddasa su da masu haddasa su da yadda za a yi a rage su.

    27 min
  • Yadda Cin Hanci Da Rashawa Ke Kassara Rayuwar Al'umma


    Ko kun san cewa da dama daga cikin matsalolin da talakan Najeriya ke fuskanta a yanzu haka cin haanci da rashawa ne suka haddasa su?

    A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya yi nazari a kan alakar wadannan abubuwa - wato cin hanci da rashawa da kuma bakin talaucin da wahalar da al'umma ke fama da su.

    Ku biyo mu don jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.

    35 min
  • Yadda kwacen waya ke ajalin jama'a a Najeriya



    A wasu sassan Najeriya, rike wayar salula kan zama hadarin da ka iya haifar da sara ko suka ko ma mutuwa idan ajali ya yi.

    A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yadda wannan matsala ke karuwa da illar da take haifarwa da kuma hanyoyin magance ta ko kauce wa fada mata.


    32 min
  • Hidimar aure: Wa ya fi jin jiki tsakanin dangin ango da na amarya?

    Sau da yawa, iyayen yarinya kan dage ranar aure saboda ba su kammala shirye-shiryen biki ko sayen kayan daki ba.

    Samari da dama kan bayar da uzuri cewa tsarabe-tsarabe - kama daga dukiyar aure, zuwa ga sadaki zuwa ga lefe - sun yi yawa shi ya sa suka kasa aure.

    Wai shin, a tsakanin dangin amarya da na ango, wa ya fi shan wahala ko kashe kudi yayin bikin aure?

    Wannan ne batun da shirin Daga Laraba ya yi nazari a kai a wannan karon.

    24 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…