
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Daga Laraba ya yi duba na musamman a kan dalilan da ke sa mace ko hana ta fara neman na da miji aure idan har yana da nagartar da ta dace da zabinsu na abokin rayuwa.
Me ya sa ita mace jira take yi sai an zo? Ba a taba yi ba ne a tarihin magabata?
Saurari cikakken shirin domin jin amsoshin wadannan tambayoyin.
Yin watsi da tarbiyar ’ya’ya na daga cikin abubuwan da suka haifar da rigingimun da ke addabar al'umma.
A karo na biyu, shirin Daga Laraba ya duba wannan al’amari.
Yin watsi da tarbiyar 'ya'ya na daga cikin abubuwan da su ka haifar da rigingimun da ke addabar 'yan Najeriya.
Shirin Daga Laraba ya duba wannan al'amari
Jama'a da dama na mamakin yadda 'yan Najeriya basa kishin kasarsu. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado dalilan da suka harzuka da yawa daga cikin 'yan Najeriyan har aka wayi gari kasar ta fita daga ransu.
Wasudai na ganin soyayya tana wanzuwa idan kowane bangare na amfana, amma 'yan Najeriya sunce manyan kasar ba ta su sukeyi ba.
Ayi Sauraro lafiya.
Yaya za ki ji idan, ana saura kwana kadan a daura aurenki, angon ya ce ya fasa saboda an turo mishi wani sako da ke nuna wani aibi da bai sani ba game da ke? Kuma me ya sa?
Mai yiwuwa tunani na farko da zai zo zuciyarki shi ne, wane ne ya yada wannan karyar a kanki?
A zamanin nan, labaran karya na yaduwa kamar wutar daji, yana kuma haddasa rudani a rayuwar mutane da dama.
Camfi wani abu ne da mutane a ko wanne bangare na duniya kan yi amanna da shi kuma ya zama bangare na al'ada.
Mene ne asalin camfi? Zai iya fita daga zukatan mutane kuwa?
A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi nazari a kan camfi da tasirinsa a rayuwar al'umma.
Yaran da ake kaiwa birni da sunan aiki na cikin halin ni-'yasu - abin dai ya yi kama da bauta.
Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) shiyyar Arewa Maso Yamma ta ce ta ceto mutum 638 da ake bautatarwa a cikin wannan shekarar.
An jima ana takun saka tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, da wani bangare na al'umma bisa zarge-zarge ko korafe-korafe daban-daban.
Daya daga cikin zarge-zargen shi ne na bata tarbiya.
Ko me ya sa har yanzu masu harkar suka kasa sauya ra’ayoyin jama’a game da wannan zargi?
Ku biyo mu ku ji yadda Dokta Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi ragargaza, da kuma yadda Ali Nuhu ya kare masana'antar.
Idan kuna biye da mu a shirye-shiryenmu biyu da suka gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye, sannan muka duba wadanda ke amfana da harkar shaye-shayen a Najeriya.
A wannan karon kuma mun mayar da hankali ne a kan rawar da ake zargin ’yan siyasa na takawa wajen gurbata wa matasa tarbiyya, da lalata musu makoma ta hanyar saka su shaye-shaye don su cimma wata manufarsu ta siyasa.
A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye da yadda ta addabi al'umma a Najeriya.
A wannan karo za mu duba mu ga shin su wane ne suke amfani da kayan maye?
From the publisher's feed
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…