Daga Laraba
Download on the App Store

Daga Laraba episodes

  • Yadda Ake Gane Labaran Karya

    Ta wace hanya mutum zai gane labarin karya a kafar intanet ko kuma a kafofin sada zumunta?

    Wani lokaci bambance labaran karya abu ne mai sarkakiya ta yadda hatta amintattun kafafen yada labarai kan fada a tarko,  su dauke su a matsayin sahihan labarai.

    Tambayar da ke yawan ci wa jama’a da dama tuwo a kwarya ita ce, ta yaya mutum zai gane labarin karya?

    Shirin Daga Laraba na tafe da bayanan hanyoyin gane labaran karya da zarar an yi ido hudu da su.

    31 min
  • Hanyoyin Da Illar Labaran Karya Ke Shafar Jama'a

    Makwanni biyu da su ka gabata mun karkata akalar shirin Daga Laraba zuwa batun labaran Karya. Mun dubi wadanda ke yadashi da masu kir kirarshi.

    A wannan karon, mun tura shirin gaba ta yadda mu ka dubi tasirin da illar labaran Karya ke haifarwa jama'a.

    Mun tattauna da masu yada labarai ta intanet, da 'yan siyasa da kuma masana a wannan fage domin fede biri har wutsiya.

    29 min
  • Yadda ’Yan Siyasa Ke Yada Labaran Karya Don Su Ci Zabe

    Labaran karya sun samu wurin zama a fagen siyasa, kusan ko’ina aka leka za a iske ’yan saiya na gudanar da harkokinsu ta hanyar amfani da labaran kanzon kurege a matsayin hanyar neman magoya baya da kashe farin jinin abokan hamayya.

    Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi nazari kan yadda ’yan siyasa ke amfani da kafafen sada zumunta wurin yada labaran bogi domin sace zukatan jama’a da kuma kayar lagon abokan hamayyarsu.

    28 min
  • ‘Yadda Masu Kwacen Waya Suka Kashe Dan Uwana Bayan Sun Illata Ni’

    A shirin Daga Laraba da ya gabata kun ji ta bakin wani karamin yaro mai kwacen waya da ya kashe mutum uku, ya raunata wasu akalla 25 sannan ya karbe wayoyi da dama.

    A yau kuma za ku ji yadda wata baiwar Allah ta safe wata 10 tana fama da irin lalurar da ta samu a sakamakon harin da masu kwacen waya suka sumar da ita sannan suka kashe dan uwanta.

    31 min
  • Yadda Masu Kwacen Waya Ke cin Karensu Babu Babbaka A Kano

    Waya na daya daga cikin abubbuwan da ake saurin sacewa amma a fakaice, saboda in a ka kama barawon waya, to yana dan dana kudarshi.

    Sai dai wani babban abun mamaki shine yadda birni kamar Kano, mai yawan al’umma da tarin jami’an tsaro, ya tsinci kanshi a cikin mawucyacin hali saboda aika-aikar masu kwacen waya a bainar jama’a dare da rana

    Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya zaga birnin Kano domin bin diddigin matsalar, da kuma gano masu aikata laifin, abin da ke sa su, da kuma wuraren da aka fi yin wannan kazamar harka.

    29 min
  • Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a rayuwar al'umma

    Samuwar fasahar sadarwa ta zamani ta fadada damar da mutane suke da ita ta samarwa da kuma yada labarai ta hanyoyin zamani musamman kafofin sada zumunta.

    A hannu guda kuma hakan ya haifar da fantsamar labaran kanzon kurege da a wasu lokuta suke yin illa ga mutuncin jama'a har ma da tayar da zaune tsaye.

     Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado yadda aka fara samun labaran bogi, wadanda suka fi yada su da kuma hanyoyin da labaran karyan ke hana ruwa gudu a cikin al'umma.

    A yi sauraro lafiya.

    31 min
  • Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci

    Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21.

    Alakar mutane da harkokin sadarwa ta zamani ta sa kusan harkokin kasuwanci sun tasamma komawa intanet, a wasu lokutan kuma ana amfani da wayar tarho ne wurin assasa harkokin kasuwanci da kuma tabbatar da su. 

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi waiwaye kan irin halin ni-’yasun da harkokin kasuwancin suka shiga a sakamakon rufe layukan sadarwa a kwanakin baya a Jihar Katsina.

    29 min
  • Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a

    So da dama bayan an kammala jefa kuri’u, masu zabe kan dakata su ga abin da zai ture wa buzu nadi – suna kasawa su tsare, a kirga, a kuma sanar da sakamako.

    Hakan na faruwa ne saboda wasu matsaloli da kan kunno kai bayan an gama kada kuri’u, wani lokaci har a yi ta kai ruwa rana. Don haka masu zabe ke son su san ko ’yan takarar da suka zaba sun kai bantensu.

    Shirin Daga Laraba na yau za ku ji irin abubuwan da ke biyo bayan jefa kuri’a, kama daga kidaya kuri’u, har ma da dalilan da zabe ke kasancewa inkonkulusib.

    24 min
  • Yadda Za A Magance Matsalolin Ranar Zabe

    ’Yan Najeriya na fuskantar matsaloli da dama a lokacin zabe, musamman ranar zabe, duk kuwa da cewa za a iya magance matsalolin idan aka bi hanyoyin da suka dace.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon, ya zakulo irin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zabe da kuma hanyoyin da za a bi domin warware su.

    31 min

About Daga Laraba

From the publisher's feed

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…