
Sign up to save your podcasts
Or


To amma nauyin hakan ya rataya a wuyan namiji ne ko mace?
Shirin Daga Laraba na Yau, ya yi nazari akan ko ya kamata mata su riƙa yiwa mazajen su wanki a matsayin wajibi ko kuma kyautatawa.
Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa jama’a masu injin Janareta a gida da wuraren kasuwanci sauya masa tsari ya koma amfani da Gas na girki. Wannan dai wata fasaha ce da wasu mutane suka ƙirƙira bayan sun yi nazari a kai.
A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba alfanu ko akasin hakan da za a iya samu gameda wannan sabon salo da aka ƙirƙira.
Daga cikin ‘yan Najeriya musamman matasa akwai da dama da ke da burin guduwa daga Najeriya zuwa kasashen Turai ko na Larabawa, ido rufe.
Ko masu irin wadannan burika sun san abubbuwan da ke tattare da zama a kasar da ba taka ba?
A wannan karon, mun dubi yadda matasa ke hankoron tafiya wadansu kasashe neman arziki ido rufe. Mun ji dalilansu, mun kuma ji ta bakin wadanda suka samu tsallakawa, sannan mun tuntubi ta bakin masana kan alfanu da kuma hadurran da ke tattare da irin wannan tafiya.
A yayin da ake bikin babbar Sallah a Najeriya da sauran ƙasashen Musulmin duniya, shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi yadda al'adun bikin sallah suka canza zuwa wani abu na daban.
Mene ne dalilan da al'adun bikin sallah suka lalace a kasar Hausa?
Saurari bayanai daga bakin dattawa, masana, da kuma matasa kan wannan maudu'i na lalacewar al'adun bikin sallah.
Batun bada rancen kudin karatu ga daliban jami'o'i na matakin digiri a Najeriya na ci gaba da daukar hankalin 'yan ƙasar.
Wace fahimta 'yan Najeriya su ka yi wa wannan batu na bashin kudin karatu ga dalibai masu neman digiri?
Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin martanin 'yan Najeriya kan wannan batu da kuma matsayin kungiyar ASUU.
Kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya da aka fi sani da NGO na neman hana mata zaman aure a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ko ta wadanne hanyoyi wadannan kungiyoyi na NGO ke shiga sha'anin zamantakewar aure?
Saurari shirin Daga Laraba domin jin inda gizo ke saka.
Tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya ya bayyana cewa babu tallafin mai a cikin kasafin kudin da ya gada da zai kama aiki daga 1 ga Yunin da muke ciki, saboda haka batun tallafin mai ya tafi ke nan.
Ko ta wadanne bangarori cire tallafin mai ya shafi rayuwar 'yan kasar?
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai daga bakin wadan da cire tallafin mai ya shafi rayuwarsu kai tsaye, da kuma bayanan masana kan wannan batu.
Litinin 29 ga watan Mayun 2023 aka rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya bayan sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben da aka yi ranar 25 ga Fabrairun wannan shekara.
Shin wadanne abubuwa al'ummar Arewacin Najeriya ke fata sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi musu?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da wadansu 'yan Arewacin Najeriya daga Jihohi 7. Ga yadda tattaunawar ta kasance. A yi sauraro lafiya.
Matsalar rashin zaman lafiya da tausayin juna a tsakanin ma'aurata a wannan zamani daya ne daga cikin matsalolin da ke ciwa mutane da dama tuwo a kwarya, lura da cewa, wadannan matsaloli na zama sanadiyyar mace-macen aure.
Shin ko kun san baya ga matsalolin da ke samo asali daga ma'aurata da abokan huldar su akwai sako-sako da walittaka a cikin musabbaban tabarbarewar zamantakewar ma’aurata da lalacewar aure a wannan zamani?
Binciken Shirin Daga Laraba na wannan mako ya gano sako-sako da walittaka a wannan zamani na daya daga cikin dalilan tabarbarewar zamantakewar ma’aurata da lalacewar aure a wannan zamani.
A da, ba a san ‘ya’yan Hausawa da shiga kungiyar asiri ba, sai dai wasanni irin su dambe da farauta da kokawa da sauransu.
Mene ne ya canza yanzu aka fara samun ‘ya’yan Hausawa a kungiyoyin asiri?
Shirin Daga Laraba na wannan Mako ya dubi yadda ‘ya’yan Hausawa suka fadawa kungiyoyin asiri a kudancin Najeriya.
From the publisher's feed
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan…