An zaɓi shugaban Sierra Leone, Julius Maada Bio a matsayin shugabanta ECOWAS CEDEAO, bayan ƙarewar wa’adin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya jagorance ta karo biyu.
A lokacin babban taron ƙungiyar karo na 67, ta amince cewa yankin yammacin Afrika matsala tsaro ta yi masa ƙamari, sai dai kuma bata taɓo batun alaƙarta da ƙungiyar ƙasashen AES da ta haɗa da Burkina Fasa da Mali da kuma Nijar waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soja.