Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda ya ke tattaunawa game da wani matashin Injiniya da ya kera motoci masu amfani da hasken rana. Abubakar Mustafa Gajibo da ya fito daga jihar Borno ya kera motocin da dama kuma tuni jama'a suka fara amfani da motocin kamar yadda za ku ji cikin shirin kashi na biyu.