Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.... more
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 176 episodes available.
January 24, 2026Menene yake haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin ɗan AdamShirin tambaya da amsa na wannan mako zai fara ne da bayani akan abinda ke haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin mutum. Sai kuma tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan yaushe aka fara taron duba lamuran tattalin arziki na Duniya da ake kira Davos world economic forum kuma wane tasiri yake da shi ga duniya da kuma yankin mu na Afirka. Sai kuma tambayarmu ta gaba wadda ke buƙatar ƙarin haske kan irin gudunmawar da ake la’akari da su kafin a ba wa mutum kyautar lambar yabon zaman lafiya ta duniya wato Nobel peace price, kamar yadda aka baiwa ƴar ƙasar Venezuela Maria Corina Machado. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...more22minPlay
January 17, 2026Me ya sa darajar kuɗaɗen wasu ƙasashen larabawa su ka fi na Amurka daraja?Shirin tambaya da amsa da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu su ka aiko mana, mu kan mika wadanan tambayoyi ga masana domin baku amsar da ta dace...................more21minPlay
January 10, 2026Tambaya da amsa: Ko ta yaya ake gane ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa?Shirin Tambaya da amsa tare da Nasiru Sani a wannan makon ma bai yi ƙasa a gwiwa ba, inda ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana kamar yadda aka saba. A cikin shirin za ku ji amsar tambaya kan irin hikimomin da ake amfani dasu dasu ne wajen gane Bunkasar tattalin arzikin ƙasa. Sai kuma amsa kan wannan tambaya da ke cewa: ko me ke haddasa kamuwa da cutar Amosanin Makogwaro wato Strep throat infection kuma mene ne alamunta? Ku latsa alamar sauti don jin amsar waɗannan dama wasu ƙrin tambayoyin da aka tattauna akansu cikin shirin....more22minPlay
January 03, 2026Ko shan magani na yiwa ɗan Adam illa ?A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako daga sashen hausa na Rfi,shin ko gaskiya ne duk magani da mutum ya sha ya na da tasa illar da zai masa? Nasiru Sani ya tunttubi masana a kai..... ...more22minPlay
December 20, 2025Tarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundationTarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundation dake taimakawa a harkar manoma a Najeriya, wai shin da gaske ne kungiyar daga Japan aka kafata kuma wanene ya kafata? Akan wannan tambaya ce muka zanta da Dr Abdulhamid Gambo mataimakin shugaban SASSAKAWA Foundation a Najeriya....more21minPlay
December 06, 2025Tambaya da Amsa: Taƙaitaccen tarihin Marigayi Sheikh Ɗahiru BauchiShirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko, inda a yau guda cikin tambayoyin da wannan shiri ya amsa shi ne buƙatar taƙaitacce tarihin fitaccen Malamin Islaman nan a Najeriya kuma jigo a Dariƙar Tijjaniya, shehu Usman Dahiru Bauchi wanda Allah ya yiwa rauswa a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da muke ta 2025 . Don samun amsar wannan tambaya ce wakilin RFI a jihar Bauchin Najeriya Ibrahim Malam Goje ya zanta da Dr Fathi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, daya daga cikin 'ya'yan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, kuma daya daga cikin wadanda suka taɓa rubuta littafi a kan marigayin. Ku latsa alamar ƙari don jin amsar wannan tambaya da sauran tambayoyin da ke ƙunshe cikin wannan shiri tare da Nasiru Sani....more21minPlay
November 29, 2025Tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan DharmendraShirin tambaya da amsa na wannan mako ya mayar da hanakali ne a kan tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan wato Dharmendra wanda ya rasu a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2025....more21minPlay
November 22, 2025Abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin numfashi wato AsthmaShirin Tambaya da Amsa na wannan mako, zai fara ne da bayani dangane da abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin shaƙar numfashi wato Asthma a turance. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Nasiru Sani.......more21minPlay
October 18, 2025Abubuwan da ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin magance matsalarShirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsara tambaya akan abinda ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin da ya kamata abi wajen magance matsalar. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Nasiru Sani..................more20minPlay
October 11, 2025Ƙarin bayani akan adadin Nahiyoyin duniya da kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasaShirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsa tambayoyin da ke neman karin bayani akan inda tsakiyar Najeriya ya kasance, da tambayar da ke neman sanin Nahiyoyi nawa ne a duniya kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa sannan wacce ta fi yawan mutane? da kuma tambayar da ke cewa, don Allah ku tambaya mana masana tattalin arziki akan mece ce TIN number kuma ina ake samunta sannan mene ne aikinta a Najeriya? Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin................more20minPlay
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 176 episodes available.