Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.... more
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 159 episodes available.
May 03, 2025Mecece hukumar raya kasashe ta USAID? Me yasa Trump ya soketa?Shirin TAMBAYA DA AMSA na wanan rana tareda Nasiru Sani, cigaba ne na tarihin Sarkin Musulmi Muhammed Bello da kuma wasu karin tambayoyi na masu sauraro suka aiko mana. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin.......more21minPlay
April 19, 2025Tasirin matakin matatar man Ɗangote ga hada-hadar makamashi a NajeriyaShirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani bisa al'ada kan kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da ku masu sauraro kuka aiko mana. A yau shirin Tambaya da Amsa zai amsa tambaya wani mai sauraro ne wanda ke neman sani ko kuma ƙarin bayanai game da tasirin matakin matatar man Dangote na daina sayar da ɗanyen mai da Naira, ga tattalin arziƙin ƙasar da kuma yadda hakan zai shafi ɗaiɗaikun jama'a.Don jin amsar wannan tambaya da kuma ƙarin wasu da shirin ya amsa a wannan mako, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....more21minPlay
April 06, 2025Shirin Sallah na musamman akan muhimmancin azumi ga musulmiKasancewar Azumin na watan Ramadan ya kunshi ladubba da tarin alkhairi a cikinsa, waɗanda suka haɗa ƙara kusanci ga mahalicci ta hanyar gudanar da ɗumbin ibadu da kyautatawa juna da nisantar dukkanin ayyuka ko lamura da suka saɓawa shari’a. Watan na Ramadan wata ne mai matuƙar daraja wanda dukkanin musulmi ke neman falala daga Allah a cikinsa, wakimmu na jihar Bauchi a Najeriya Ibrahim Malam goje ya zanta da Shehin Malami Imam Muhammad Hadi Abubakar, Na'ibin Babban Limamin Masallacin Juma'a na At-Taqwa, da ke garin Bauchi dangane da muhimmancin watan na Ramadana....more20minPlay
April 05, 2025Bayani akan tsarin ra'ayin riƙau a siyasar DuniyaA yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne dangane da ra’ayin riƙau a fagen siyasa wanda jama’a da dama ke neman bayani akansa....more20minPlay
March 22, 2025Tarihin ƙungiyar ECOWAS da kuma tasirin ta ga ƙasashe mambobintaShirin ‘Tambaya Da Amsa’,shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma a kowane mako yake zuwa muku,a yau shirin tambaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yadda ƙungiyar ECOWAS ta kafu da kuma tasirin ta ga ƙasashe mambobinta....more21minPlay
March 15, 2025Me ye ma'anar kalmomin Kano da Katsina?Shirin TAMBAYA DA AMSA da wanan mako tareda Nasiru Sani ya kuma amsa tambaya da wasu suka aiko mana kan muhimmanci Garin Goma na Jamhuriya Dimokradiyar Congo ga 'yantawayen M23. Ku latsa alamar sauti domin jin karin bayani...more19minPlay
February 22, 2025Faduwar gaba?Jin tsoro ne ko kuma wata alama ce ta gazawar zuciya?Tambaya da Amsa,bisa al’adar shiri ne da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, Shin kome me ke kawo faduwar gaba? Jin tsoro ne ko kuma wata alama ce ta gazawar zuciya?...more22minPlay
February 15, 2025Ko wata kasa a doron duniyar nan, ta taɓa fusƙantar irin gobarar da ta tashi a birnin Los AngelesShirin na Tambaya da amsa na baiwa masana damar kawo ƙarin haske a wasu daga ciƙin tambayoyinku daga nan Rfi,shin ko wata kasa a doron duniyar nan, ta taba fusƙantar irin gobarar da ta tashi a birnin Los Angeles na Amurka kuma duk da kasancewarta babbar ƙasa mai isassun kayan aiki,ko mai ya hana ya hana Amurka samun nasarar shawo kan gobarar a cikin ƙanƙanin lokaci...more20minPlay
February 08, 2025Tarihin kafuwar ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Rights WatchShirin 'Tambaya Da Amsa na wannan mako zai kawo muku tarihin kafuwar ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch, da kuma tarihin Gadar Jebba da ke tsakiyar Najeriya.....more20minPlay
February 01, 2025Bayanai dangane da dalilan dake sanya ci gaba ko karayar tattalin arzikin ƙasasheA yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wasu kasashen na duniya.A yau shirin tamabaya da amsa zai kawo muku bayanai ne akan yanayin tattalin arzikin Kasashen duniya da hanyoyin da kan haifar da ci gaban sa da kuma karayarsa a wasu kasashen na duniya....more21minPlay
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 159 episodes available.