
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar Borno da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.
Bayan kwashe shekaru da dama na rikicin Boko Haram da kuma tasirinsa ga tattalin arziki, gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na neman wata hanya ta bunƙasa tattalin arzikinta da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummarta.
Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ta haɗu da masu zuba jari da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a wani taro da aka gudanar a Legas, domin duba damar zuba jari da za ta taimaka wajen samar da abin da ake kira durable solutions, wato hanyoyin magance matsalolin al'umma na dogon lokaci.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta sanar da cimma alkawuran zuba jari har guda tara bayan kammala taron tattaunawa da aka gudanar a Legas
Kamfanin Dangote ya ware hannun jari na darajar Naira miliyan 366 domin taimakawa ‘yan gudun hijira da waɗanɗa suka dawo gidajensu, tare da yin alkawarin bayar da tallafin karatu ga ‘yan mata 6,000.
Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata.
Madallah!
Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har yanzu babu wani alamun sauƙi.
A kasuwanni, farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da kasancewa babban ƙalubale, yayin da ’yan kasuwa ke kokawa da tsadar sufuri da wutar lantarki..
Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya.
Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya.
Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gargaɗi, ta hanyar dakatar da lodi ko sayar wa kamfanoni baraguzai da suke tattarawa.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance.
Matatar ta sanya hannun jari biliyan 4 da miliyan 100 kasuwa, kan Naira 525 ga kowane guda, inda take fatan tara kusan Naira tiriliyan 2 da biliyan 150.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..............
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........
Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani.
Kalaman Atiku, sun tayar da kura tare da ƙara zafafa lamura a fannin siyasa da tattalin arzikin ƙasar, inda a ƙarshe, shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kansa, ya fito ya soki lamarin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba...............
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma tattalin arzikin ƙasar?
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmad Abba............
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?
A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau.
Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a fannin tattalin arziki.
Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40.
Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners