Kasuwanci

Kasuwanci

By RFI HausaBusiness
Download on the App Store

Kasuwanci episodes

  • Mahangar masana kan kiran IMF da bankin Duniya ga Najeriya don sauƙaƙa tsadar rayuwa

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin al’umma ta amfana a zahiri da kuma ci gaban tattalin arziki ƙasar.

    Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, sun bayyana cewa har yanzu tattalin arziƙin Najeriya bai kai matsayin da za a ce ya daidaita ba, duk da wasu sauye – sauye da gwamnati ke aiwatarwa. Hukumomin sun ce rashin daidaiton tattalin arziƙin na ci gaba da shafar rayuwar jama’a, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki.

    Masana tattalin arziƙi sun goyi bayan gargadin da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, ya yi kan cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a ƙasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar barazana idan ba a tabbatar da dorewarsu ba.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Yadda Najeriya ta yi iƙirarin rarar tiriliyan 12 a watanni 6 farkon 2025

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali kan ikirarin gwamnatn Najeriya na samun rarar kuɗi da ya kai tiriliyan 12 kuma kashi 21 daga ciki ta same su ne daga bangarorin da ba na man fetur ba a cikinn watanni 6 na farkon shekarar 2025.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Hangen masana tattalin arziƙi kan sabon harajin gwamnatin Najeriya

    Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta.

    Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon da ya gabata dangane da wannan dokar haraji wadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da suka akanta.

    A cikin shirin akwai tattaunawa da ƙwararru a fagen na tattalin arziƙi waɗanda da dama suka yi suka ga sabon tsarin harajin na shugaba Tinubu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Abubuwan da sabon tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa

    A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa.

    Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin da ake sa ran za ta sauya fasalin tsarin karɓa da tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnati daga ɓangaren haraji a Tarayyar Najeriya.

    11 min
  • Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar.

    Samun damar aika kuɗaɗe ta hanyar amfani da manhajojin wayar hannu ba tare da yankar kuɗin haraji masu dama ba, dai tuni ya kawo sauyi dangane da hada-hadar kuɗi a Jamhuriyar ta Nijar, lamarin da ya zo a daidai lokacin da aka takaita fitar da kuɗaɗe daga Bankuna bayan juyin Mulki, tsarin da ya sa mutane da dama masu asusun ajiya a bankuna rungumar mahajojin na zamani a matsayin sabbin wuraren adana kuɗaɗen nasu. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........

    11 min
  • Majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yawaitar harajin Bankuna

    A 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan karon, ya mayar da hanhali ne kan binciken da Majalisar Walikan Nigeria ta ƙaddamar dangane da ƙorafin ƴan ƙasar kan maban-banta haraji da Bankuna ke yawaita cirewa a asusun ajiyarsu.

    A ƙarshen watan oktoban da ya gabata ne, Mjalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin da ta dorawa alhakin bin diddigin korafe-korafen da masu ajiya a bankuna ke yi kan yawan cire musu kudade da ake yi daga asusun ajiyarsu na banki.

    Kaddamar da kwamitin, ya biyo bayan tarin korafe korafen da ƴan Nigeria ke yi, musamman masu ajiyar kudi a bankunan kasar, game da yawan cire musu kudade ba-gaira ba dalili da bankunan ke yi, da sunan wasu ayyuka da bankunan ke ikirarin gudanarwa.

    Masana na alakanta wannan batu, da nau’o’in harajin da ake da su a kasar, a matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, yayinda wasu ma’aikatan gwamnatin kasar, ke kukan cewa wasu kudaden da ake cire musu, musamman na gidaje da na pansho, ba a tura su ga hukumomin da suka dace.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

    11 min
  • Tasirin ƙarin harajin kashi 15 da Najeriya ta sanya kan man da ake shigarwa ƙasar

    Shirin a wannan makon ya yi dubi ne akan batun sabon harajin kashi 15 da gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanya kan tataccen man fetur da dangogin sa da ake shigo da su ƙasar daga ketare, ala’marin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar kan yuwuwar tashin farashin litar man na fetur.

    A ranar Jumma’ar da ta gabata ce, fadar gwamnatin Najeriya, ta sanar da cewa tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da harajin fito na kashi 15 kan man fetir da dizal da za a shigo da su ƙasar daga waje, yana mai bayyana tsarin, a matsayin matakin bunƙasa matatun mai na cikin gida da kuma dogaro da kai a fannin makamashi.

    Sai dai, tuni dilllalan man fetur a ƙasar suka fara gargaɗin cewar muddin karin ya tabbata to akwai yuwuwar farashin man fetur da dangoginsa ya yi tashin da zai fi ƙarfin da yawa daga cikin al’ummar ƙasar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

    11 min

About Kasuwanci

From the publisher's feed

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

More shows like Kasuwanci

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners