
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a.
Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada da su a cikin ƙasa tare da waɗanda jama’a ke jujjuyawa a hannunsu.
Adadin wannan kudi dai a cewar bankin na CBN, ya kai Naira Triliyan 123 da biliyan 15, a watan Fabareiru, inda aka samu raguwar adadin madarar kuɗi da ke hannun jama’a akan na watan Janairu, wanda ya kai Nera Triliyan 123 da biliyan 36.
Haka ma adadin kudaden kasar a asusun ajiyarta na ketare ya ragu zuwa Nera Triliyan 28 da biliyan 41 daga Nera biliyan 29 da biliyan 61.
Ku latsa alamar sauti don sauti don sauraron cikkan shirin tare da Ahmad Abba.............
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka.
Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka.
To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla.
A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan al’amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo.
A makon jiya, shirin ya tattauna wannan batu ne da malaman da muka gayyato, wato Dr. Aminu Idris Harbau masamanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya, da Dr. Ibrahim Adamu na sashin nazarin yankin gabas ta Tsakiya a jami’ar Havard da ke Dubai na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai Mohammad Qaddam Sidiq Isa, mai sharhi kan al’amuran Yau da Kullum shima a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai kuma Isma’il Albabawee ɗan jarida kuma ɗalibi a jami’ar Karbala a ƙasar Iraki.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar diflomasiyya a bikin baje kolin sabuwar shekarar kalandar kasar China da aka gudanar.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu.
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar.
Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan Kwastam da ke Maitama a Abuja.
Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce.
Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka zirga-zirga a kayan a iyakokin kasashen biyu ciki harda jigilar man metur na kamfanin Dangote, hakazalika za’a bada damar wucewar wasu kayayyaki da suka makale a bodar Kamba na jihar Kebbi, tireloli 1,600, da suka kwashe sama da watanni 2.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram.
Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba’a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India.
Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suka kaɗai suka mamaye kusan kashi 25% na jimillar hada-hadar kasuwancin cikin gida na duniya da kuma cinkayyar mutane biliyan biyu.
Domin ko a shekarar 2024 kaɗai, an yi cinikin sama da Euro biliyan 120 a tsakanin ɓangarorin biyu.
Masu sharhi na ganin cewa kalaman wannan yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba.
Yarjejeniyar dai na nufin cewa daga yanzu, India za ta soke ko kuma zaftare haraji kan hajoji da dama da take shigarwa yankin Turai, da suka haɗa da motoci daga kaso 110% zuwa 10% kachal, matakin da zai shafi kayan abinci da barasa da tufafi da kayan ado da dai sauransu.
An dai ƙulla yarjejeniyar ce a daidai lokacin da mafi yawan ƙasashen duniya ke takun-saka da Amurka sakamakon haraji babu ƙaƙƙautawa da Donald Trump ke amfani da shi don tursasawa abokan hulɗa.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners