
Sign up to save your podcasts
Or


'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'.
An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.
Da yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa.
Mawaƙin ya taka gagarumar rawa sakamakon waƙokinsa na siyasa da na gargajiya, da noma da kuma zamantakewa, lokacin da ya yi zamaninsa a shekarun 1960 zuwa 1980.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya.
A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin masana a ɓangaren al'adu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa.
Ku danna alamar sautin da ke sama domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa...........
Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa.
Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi.
A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen Hausa da sauya salon magana don juyata zuwa nishaɗi.
Sai dai bincike ya nuna cewa wannan daɗaɗɗiyar al'ada tana dab da ɓacewa gaba ɗaya a wannan zamanin na yanzu.
Babban dalilin da ya sa sana'ar ke mutuwa shi ne rashin gado, domin kuwa ko da su kansu 'ya'yan mawaƙan na 'Yan Kama ba sa sha'awar ɗaukar wannan sana'a don gadon iyayensu kamar yadda aka saba a baya.
Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa
Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure.
Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar.
Irin wannan bincike, ya taimaka matuka wajen tantance masu neman aure tare da dakile wadanda ke da matsaloli a fannin dabi’u, rashin halayen kwarai da kuma matsala a fannin lafiya.
Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida.
Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya.
Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama a ƙasa mai tsarki sakamakon yawaitar Hausawa ko dai ƴan safara ko kuma masu Ibada koma mazauna wannan ƙasar ta Saudiyya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
From the publisher's feed
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners