Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

By RFI Hausa
Download on the App Store

Al'adun Gargajiya episodes

  • Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu

    Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.

    10 min
  • Bikin cika shekaru 10 da faro bikin ranar Hausa ta duniya

    Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya tattauna ne a kan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.

    Fitaccen ɗan Jarida daga Najeriya Abdulbaqi Aliyu Jari shi ne ya jagoranci assasa wannan rana mai muhimmanci ga Harshen Hausa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman...............

    11 min
  • Yadda zamani ke tasiri akan salon magana a tsakanin al'ummar Hausawa

    Shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda zamani ke tasiri kan salon magana ko 'Gagara Gwari' a tsakanin al'ummar Hausawa, musamman ma matasa. Masana wannan harshe da dattawa cikin al'ummar sun yi fashin baki akan dalilan da suka sanya wannan salo na zance wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa, da gudummawar da kowane ɓangare ke bayarwa wajen wannan matsalar.

    11 min
  • Yadda al'adar bikin cika ciki ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa

    Shirin na wannan mako ya yi duba ne kan al'adar nan da ta jima tana cin kasuwa a ƙasar Hausa, wato Sallar cika ciki da ake gudanarwa bayan Sallar layya.

    Tsawon shekaru da wannan al’adar ta dore,ake kuma ci gaba da gudanar da ita a wurare da dama.

    Al'ummar Hausa da dama a birane da karkara a duk ranakun tara da goma ga watan farko na shekarar musulunci  wato Muharram, sukan gudanar da azumin da kuma raya al'adar nan mai suna cika ciki wato dai sai kaci ka koshi kuma abinci mai dadi, wasu kan amfani da iya abinda suke da shi, yayinda wasu suke karawa da hidindimu.

    Wani abin lura shine, yadda a yankunan karkara, idan wannan lokaci ya ƙarato, jama’a musaman mata na dukufa ne ɓangaren girki, inda a wajen gida yara matasa kan ɗora sanwa wasu lokutan su kan yi amfani da haka wajen raya al’adar nan da aka sani da  aci a cika ciki sannnan ga nishaɗi. 

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Tasirin al'adar ''Mai suna'' ko Takwara ga ƙabilar Kanuri a Jamhuriyyar Nijar

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali ne kan guda cikin al'adun Ƙabilar Kanuri can a kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, Al'adar da ake yiwa laƙabi da ''Mai suna'', al'adar da ke da matuƙar tasiri a cikin wannan ƙabila da ke da matuƙar yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru.

    Al'adar ta Mai suna ko kuma takwara, na cikin al'adu masu matuƙar girma a wannan ƙabila da kuma ke da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƴan uwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Yadda aka gudanar da bikin al'adun Dukkawa

    Shirin al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya maida hankali  a kan bikin al'adun Dukkawa na wanan shekara ta 2025  wanda ya gudana a jihar Neja da ke Tarayya Najeriya.

    Ku shiga alamar sauti domin sauraron  cikakken shiri.......

    10 min

About Al'adun Gargajiya

From the publisher's feed

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin…

More shows like Al'adun Gargajiya

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners