Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 208 episodes available.
August 18, 2025Yadda wasanni suka gudana bayan fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a TuraiShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya mayar da hankali ne a kan yadda aka fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a bana a manyan Lig-Lig na sassan nahiyar Turai. Manyan wasannin dai sun haɗa da na Firimiyar Ingila, La Ligar Spain, da kuma gasar Ligue 1 na ƙasar Faransa. Kamar yadda za a ji cikin shirin tare da Khamis Saleh, Liverpool ce ta fara buɗe sabuwar kakar wasa a Firimiyar Ingila inda ta lallasa Bournemouth da ƙwallaye 4-2....more10minPlay
August 11, 2025Yadda wasanni ke ɗaukar hankalin matasa a lokacin hutu a NijarShirin a wannan makon zayyi duba ne kan yanda wasanni ke ɗaukan hankalin matasa a irin wannan lokaci na hutun ƴan makaranta a Nijar. A duk lokacin da aka yi dogon hutun ƴan makaranta a Jamhuriyar Nijar, wanda ke farawa daga watan Yuli zuwa Satumba. Irin wannan lokaci na zama wata babbar dama ga masu kula da ɓangaren wasanni iri daban daban, don suna samun ɗinbin matasa da ke nuna sha’awarsu a ɓangaren wasanni....more10minPlay
August 04, 2025Yadda shugaban Najeriya ya tarbi tawagar Super Falcons bayan lashe gasar WAFCONShirin a wannan makon zayyi duba ne kan karramawar da gwamnatin Najeriya ta yi wa tawagar Super Falcons na lashe gasar WAFCON. A makon da ta gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan tawagar ƙungiyar kwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Falcons, bayan nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10 daga cikin 13 da aka yi. Cikin kyautukan da gwamnati ta baiwa waɗannan ƴan wasa akwai lambar girmamawa na ƙasa wato OON da shugaban Tinubu ya baiwa dukkan ƴan wasan da masu horar dasu, hakazalika kowacce ƴar wasa ta samu dalan amurka dubu 100, da kuma karin naira miliyan goma-goma daga ƙungiyar gwamnonin Najeriya. Tuni dai shugaban hukumar wasani a Najeriya Shehu Dikko ya yaba da wannan nasarar da kuma irin karramawar da shugaban ƙasar ya yiwa ƴan wasan. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....more10minPlay
July 28, 2025Yadda ta kaya a gasar lashe kofin Afirka ta mataShirin Duniyar Wasanni a wannan makon tareda Khamis Saley yayi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar lashe kofin mata ta Afrika WAFCON da aka yi a ƙarshen mako. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.........more10minPlay
July 21, 2025Yadda RFI hausa Hausa ta ƙulla alaƙa da ƙano pillarsa cikin shirin Duniyar wasanni na yau zaku ji yadda sashin Hausa na RFI ya ƙulla yarjejeniyar Naira miliyan 100 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars dake Arewacin Najeriya a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2025. A latsa alamar sauti domin domin sauraren cikakken shirin....more10minPlay
July 07, 2025Tasirin wasannin sada zumunta ga manyan ƴan wasa a lokacin hutun manyan LigShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya mayar da hankali kan wasanni da ke gudana a lokacin hutu, ta yadda manyan ƴan wasa daga lig lig na Turai da sauran nahiyoyi ke komawa gida don doka wasannin sada zumunta a irin wannan lokaci, lamarin da ke nishaɗantarwa da kuma ƙara danƙon alaƙa tsakanin manyan ƴan wasan da masu tasowa. A cikin shirin zakuji tattaunawa da masana a fannin na wasanni da kuma tsaffin ƴan wasa game da muhimmancin irin waɗannan wasanni na sada zumunta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....more10minPlay
June 30, 2025Kwara da Rivers sun lashe kofin ƙalubale na Najeriya a bangaren Mata da MazaShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali ne kan wasannin ƙarshe na gasar cin kofin ƙalubale na Najeriya, wadda yanzu ake kira President Federation Cup, da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke birnin Lagos. Da wasan mata aka fara, inda aka ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Nasarawa Amazons da ke garin Lafia da Rivers Angels ta birnin Fatakwal a wansan ƙarshe karo na 10 a wannan gasa, ɓangaren mata. Ƴan matan Nasarawa ne suka fara saka ƙwallaye biyu a ragar Rivers, ƙwallayen da Rukayyat Shola Sobowole ta ci, a yayin da Taiwo Ajibade da Taiwo Afolabi suka farke wa Rivers. Haka dai aka tashi wannan wasa biyu da biyu, Rivers mairiƙe da kofin ta sake daukawa a wannan karon a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4 da 2. Bayan wasan na mata, da baye-bayen kyautuka ne aka shiga wasan maza, inda kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United ta garin Ilorin ta doke Abakaliki FC da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da aka buga canjaras babu ci....more10minPlay
June 23, 2025Shirye-shiryen sun yi nisa na fara gasar Firimiyar Najeriya ta baɗiShirin Duniyar Wasanni a wanan mako ya yi dubu ne kan shirye-shiryen fara gasar Firimiyar Najeriya ta kaka mai zuwa, kuma tuni hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato NPFL, ta sanya 22 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar soma kaka ta baɗi. An dai ji shugaban hukumar shirya babbar gasar ta Najeriya Gbenga Elegbeleye na cewar, suna duba yuwuwar soma amfani da na’urar VAR a gasar mai zuwa, baya ga kuma inganta kayayyakin gudanarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............more10minPlay
June 16, 2025An bude gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi a AmurkaShirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana. Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri...........more10minPlay
June 09, 2025Yadda ta kaya a gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin ZazzauShirin Duniyar Wasanni a wannan makon yi duba ne kan gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin Zazzau da ke tarayyar Najeriya, inda ƙasashe 5 da suka haɗa da Nijar da Kamaru da Chadi da Burkina Faso da Mali da kuma mai masaukin baƙi Najeriya suka fafata. Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar da gasar a a birnin Zazzau bayan kwashe fiye da shekara 12 ba tare da gudanar da ita ba. A wannan karon gasar ta yi armashi sosai ganin yadda jama'a sukayi tururuwar zuwa filin sukuwan dawaki da turawan mulkin mulka suka gina fiye da shekara 100, domin gane wa idonsu yadda za ta kaya.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 208 episodes available.