Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.
July 22, 2024Shirye-shiryen gudanar da gasar olympics 2024 a Paris sun kammalaYau shirin zai yi, duba ne kan yaddata kaya a game da sshirye-shiryen gudanar da gasar olympics da za a fara a cikin wannan watann a birnin Paris. shirye-shirye dai sun yi nisa a game da wannan gasa, duba da cewa ilahirin tawagogin kasashe sama da ɗari 2 da za su fafata a wasanni dabam-dabam sun sauka a wannan birni, haka ma mabobin kwamitin shirya wannan gasa. Wani sabon al'amri kuwa shine yadda za a gudanar da bikin fara wannan gasa a cikin kogin Seine daya ratsa birnin Paris....more10minPlay
July 15, 2024Yadda El-Kanemi ta lashe kofin ƙalubale na Najeriya na farko cikin shekaru 32Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan nasarar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta El-Kanemi Warriors ta lashe kofin kalubale na Najeriya na shekarar 2024. A karshen watan da ya gabata ne dai ƙungiyar ta Jihar Borno ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya, bayan da doke Abia Warriors da ci 2 - 0 a filin wasa na Mobolaji Johnson da ke Lagos....more10minPlay
July 08, 2024An kammala gasar firimiyar Najeriya ta kakar 2023/2024Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL da aka kamala, ta kakar 2023 2024, gasar da Enugu Rangers ta lashe.To kamar yadda kuka ji tuni kungiyar Enungu Rangers ta lashe gasar Firimiyar Najeriya ta bana da aka kammala, yayin da kungiyar Remo da Enyimba suka kasance a matakin na biyu dana uku To tun bayan kammala gasar masu sharhi ke faman tabka muhawara game da yadda gasar ta gudana, Isma’ila Abba Tangalash mai sharhin ne kan lamuran wasanni, ya mana bayanin yadda gasar ta gudana a dunkule....more10minPlay
July 01, 2024Yadda sakamakon wasannin gasar kasashen Turai ke ba da mamakiShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar cin kofin Nahiyar Turai ci gaba gaba da bada mamaki, ganin yadda kananan kasashe ke doke manyan da suka yi suna a bangaren kwallon kafa a duniya. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........more10minPlay
June 24, 2024Tarihin gasar Euro da kuma wainar da ake toya wa a gasar da ke gudana a JamusShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda gasar Turai wato Euro 2024 ke gudana a kasar Jamus. gasar Euro, wacce hukumar kula da kwallon kafar Turai ke shiryawa duk bayan shekaru 4. Shirin ya yayi waiwaye kan tarihin ita wannan gasa da kuma irin wainar da ake toyawa a gasar da yanzu haka ke gudana. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........more10minPlay
June 10, 2024Fatanmu wasan Damben gargariya ya shiga wasannin Olympics - Dambe WarriorsShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan ci gaban da wasan Damben Gargajiya ke samu a kasar Hausa. Akwai kungiyoyi da dama da a yanzu suka shiga cikin sabgar wasan dambe wanda kuma hakan ke kara mata tagomashi dama jawo ra’ayin wadanda da basa ciki shiga cikinta gadan-gaban. Dambe Warriors na daga cikin kungiyoyi da ke suka jima suna shirya wasan inda 'yan wasan ke samun albashi mai tsoka a mataki daban-daban. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........more10minPlay
June 03, 2024Mahawara kan yadda kungiyar Madrid ta lashe kofin zakarun TuraiShirin Duniyar Wasanni a wannan makon, ya maida hankali ne kan wasan karshe na gasar zakarun Turai wanda kungiyar Real Madrid ta lashe karo na 15 a tarihi, bayan doke Brussia Dortmund, abunda ya maida ita kungiyar data fi kowwacce nasarar dauke wannan kofi mafi girman dearaja a Turai. Gabanin wasan dai ana ganin da wahala Madrid din ta iya samun nasara lura da yadda Dortmund ta zo matakin wasannan na karshe, duk kuwa da cewar tarihin Madrid din na nuna tafi iya lashe kofin data sha wahalar zuwa wasan karshe.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh........more10minPlay
May 27, 2024Bitar yadda aka kammala kakar wasanni ta banaShirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan yadda aka kammala gasar La liga da wasan karshe na kofin FA da sauran abubuwan da suka faru a karshen wannan mako. Haka nan shirin ya yi tsokaci game da babban wasan da za a iya cewa ya rage a nahiyar Turai a wannan kaka wato wasan karshe na gasar Zakarun nahiyar da za ayi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikken shirin tare da Khamis Saleh........more10minPlay
May 20, 2024Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jereShirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere....more10minPlay
May 06, 2024Har yanzu akwai rashin tabbas game samar da ingantaccen tsaro yayin gasar Olymics mai zuwaShirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh...more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.