
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Duniyar wasanni na wanan makon tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne akan gasar lashe ƙofin duniya ta kungiyoyi da aka bude a karshen mako a ƙasar Amurka dama sauye -sauyen da aka samu a bana.
Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shiri........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon yi duba ne kan gasar sukuwar dawaki da aka gudanar a birnin Zazzau da ke tarayyar Najeriya, inda ƙasashe 5 da suka haɗa da Nijar da Kamaru da Chadi da Burkina Faso da Mali da kuma mai masaukin baƙi Najeriya suka fafata. Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar da gasar a a birnin Zazzau bayan kwashe fiye da shekara 12 ba tare da gudanar da ita ba.
A wannan karon gasar ta yi armashi sosai ganin yadda jama'a sukayi tururuwar zuwa filin sukuwan dawaki da turawan mulkin mulka suka gina fiye da shekara 100, domin gane wa idonsu yadda za ta kaya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi duba ne kan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai da aka yi a ƙarshen mako tsakanin PSG ta Faransa da kuma Inter Milan, inda PSG ta samu nasarar lashe gasar bayan da ta zazzaga wa Inter Milan ƙwallaye biyar.
Wannan ne dai karon farko da PSG ta lashe wannan kofi, kuma karo na farko da wata ƙungiya daga Faransa ta lashe shi tun bayan Marseille a shekarar 1993.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Khamis Saleh............
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.
A wannan makon shirin zai ɗora ne akan wanda muka kawo a baya, wanda ya yi bita a game da wasu shahararun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na arewacin Najeriya da suka taimaka wajen ƙyanƙyasar fitattun ƴan wasa da suka yi shura a fagen ƙwallon ƙafa a ƙasar. Shirin ya yaɗa zango ne a Kano, inda ya gana da wasu tsaffin fitattun ƴan wasa, musamman na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Racca Rovers.
A wannan makon, shirin Duniyar Wasanni ya ɗora ne kan shirin mu daya gabata, wanda yayi duba kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimakawa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A wannan makon shirin zai yada zango ne a garin Jos na jihar Filato, wanda ke zama gida ga ƙungiyar Mighty Jets FC.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimaka wa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A baya yankin Arewacin Najeriya ne ke kan gaba wajen samar da manyan ƴan wasan da ake ji dasu a ƙasar, kuma mafi yawancin ƴan wasan sun fito ne daga ƙungiyoyi na cikin gida irinsu DIC Bees da ke Kaduna wacce ta koma Ranchers Bees da Racca Rovers da ke Kano da Mighty Jets da ke garin Jos da dai sauransu.
Sai dai shirin a wannan lokacin zai yada zango ne a jihar Kaduna, don yin duba a kan ƙungiyar DIC Bees, wacce Sanata Muktar Muhammad Aruwa ya saya a shekarun 1980, kuma ya sauya mata suna zuwa Ranchers Bees.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...........
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon, ya yi duba ne kan wasan ƙarshe da aka yi na gasar Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid, inda Barca ta samu nasarar lashe kofin karo na 32 a tarihi. Haka nan shirin ya duba nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Liverpool ta yi a wannan kaka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin masu horarwa na cikin gida a ci gaban ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka.
A baya-bayan nan ƙasashen na nahiyar Afirka sun mayar da hankali wajen ɗaukar masu horarwa na cikin gida tun bayan rawar da Morocco ta taka a gasar cin kofin Duniya ta 2022 karon farko da aka ga irin hakan daga wata ƙasa a nahiyar ta Afrika.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Ƙwallonn Kafar Afirka CAF ta gudanar da zaɓenta, inda aka sake zabar Patrick Motsepe a matsayin shugaba a karo na biyu. Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen wakilan nahiyar a Hukumar Ƙwalllon Ƙafa ta Duniya, FIFA, inda Afirka ke da wakilai 6, har da shugaban CAF mai kujerar kai-tsaye..
From the publisher's feed
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners