
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako yayi duba ne kan yadda aka kammala wasanni sojoji na nahiyar Afrika. Wannan ne dai karo na biyu da tawogogin ƙasashe 20 suka fafata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda kuma tawagar ƴan wasan sojoji ta Najeriya ta zamo zakara, bayan da ta samu nasarar lashe lambar zinari 114 da azurfa 65 sai kuma tagulla 55 a jumlace ke nan ta samu lambobin yabo 234.
Ƙasar Aljeriya ke bi mata a matsayin na 2 da lambar zinari 53 da azurfa 22 sai kuma agulla 21, a jumlace ita kuma ta samu lambobin yabo 96, Kenya ce tazo ta 3 bayan da ta lashe lambobin yabo 50.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025.
A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Algeria da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da Senegal da Masar da Equatorial Guinea da Cote d’Ivoire da Uganda da Afrika ta Kudu da Gabon da Tunisia da Najeriya.
Sauran sun ƙunshi Zambia da Mali da Zimbabwe da Tsibirin Comoros da Sudan da Benin da Tanzania da Botswana da kuma Mozambique, a wani yanayi da Bostwana ke samun tikitin gasar karon farko bayan dakon shekaru 12.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa.
Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.
Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50.
Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa.
Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da yin watsi da su a filin jirgin sama ba tare da ance kuci kanku ba.
Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....
Shirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
Shirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi duba ne kan komen da Kyaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa ya yi wa tsohon ƙungiyarsa Kano Pillars tare da abokin wasansa Shehu Abdullahi. A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne dai ƙungiyar kwallo ƙafa ta Kano Pillars a hukumance ta sanar da kulla yarjejeniyar shekara guda da ƴan wasan.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
A dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiyen wasannin sharen fagen samun gurbi a gasar lashe kofin Afrika, Hukumar Kula Ƙwallon kafar Afrika CAF ta ce filayen wasan ƙasar Ghana ba su da ingancin da ya kamata a ce an gudanar da manyan wasanni na kasa da kasa a cikin, matakin da ke kara nuna gazawar ƙasar.
Ita dai hukumar CAF ta ce ba komai ya sanyata daukar wannan mataki ba, face yadda ta ce aƙwai rashin wadatatciyar ciyawa da rashin magudanun ruwa da dai sauransu a filin wasa na Baba Yara da ke birnin Kumasi, haka ta ce abin ya ke a sauran filayen wasanni irin na Cape Coast da kuma na Accra.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
Shirin a wannan lokaci zai leka gasar Firimirar Najeriya wato NPFL Wanda aka shiga mako na uku da somawa.
Gasar Firimiyar Najeriya na daga cikin manyan gasannin Lik-lik da ake ji da su a nahiyar Afrika, musamman idan akayi la’akari da yadda ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa ke taka rawar gani a gasar zakarun Ƙungiyoyin Afrika.
From the publisher's feed
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners