Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.
April 24, 2023Halin da tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya ke cikiShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan halin kunci da wasu tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya da suka wakilci kasar a matakai daban-daban ke ciki....more10minPlay
April 10, 2023Duniyar Wasanni: Tarihin Mesut Ozil tsohon dan wasan JamusShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya duba tarihin tsohon dan wasan tawagar kasar Jamus da ya yi murabus daga buga kwallon kafa a ‘yan kwanakin nan wato Mesut Ozil....more10minPlay
April 03, 2023Tagomashin da tawagar kwallon kafar Senegal ke samu a matakin duniyaShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya yi nazari ne kan irin ci gaban da kasar Senegal ke samu a ‘yan shekarun da suka wuce a harkar wasan kwallon kafa a duniya....more10minPlay
March 27, 2023Gudunmawar Marigayi Isma'ila Mabo ga bangaren wasannin NajeriyaA farkon wannan watan na Maris ne, Nigeria ta rasa daya daga cikin zakakuran tsaffin ‘yan wasan kwallon kafa na kasar, Sama’ila Mabo, bayan jinyar da ya sha fama da ita a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, wannan shi ne maudu'in da shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali akai....more10minPlay
March 13, 2023Yadda ake ci gaba da fafata gasar Super League din kasar NigerShirin "Duniyar Wassani" na wannan makon ya leka ne Jamhuriyar Nijar inda ake ci gaba da fafatawa a gasar lik din kasar.An kammala wasan zagaye na farko a gasar lik din Jamhuriyar Niger, da kungiyoyi 14 ke fafatawa a cikin ta.Gasar ta bana ta fuskanci tsaiko da dama ganin yadda a tsakayar ta aka tafi hutu don halartar gasar CHAN, sannan kuma aka sake bada hutu ga 'yan wasa bayan kammala gasar....more10minPlay
March 06, 2023Yadda gasar Firimiyar Ghana BETPAWA ke samun koma bayaShirin mu na wannan makon zai yi duba ne akan gasar firimiyar kasar Ghana wacce ake wa lakabi da BETPAWA. A yanzu gasar ba ta cikin jerin gasannin 10 na farko a Afrika, lamarin da ya nuna irin kalubelen da ta ke fuskanta, wanda suka hada da rashin halartan filin wasa daga magoya bayan kungiyoyi da rashin masu saka hanun jari da dai sauransu ....more10minPlay
February 20, 2023Manyan kungiyoyin gasar Firimiyar Ingila na fuskantar kalubale a banaShirin Duniyar Wasanni na wannan mako ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan wasannin kwallon kafa, dangane da koma bayan da wasu daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa ke fuskanta a gasar Firimiyar bana....more10minPlay
February 13, 2023Hasashen yadda za ta kaya a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun TuraiShirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali kan wasannin zagayen kungiyoyi 16 na gasar cin kofin zakarun Turai da za a faro cikin makon nan. Ayi saurare lafiya....more10minPlay
February 06, 2023Senegal ta lashe kofin 'yan wasan cikin gida na CHAN bayan doke AlgeriaShirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan gasar lashe kofin Afrika ta 'yan wasan cikin gida wato CHAN wadda Senegal ta lashe a yanzu....more10minPlay
January 30, 2023Yadda gasar kwallon dawaki ke ci gaba da samun karbuwa a sassan NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan wasannin kwallon dawaki ko kuma Polo, guda cikin wasannin da ke dimbin magoya baya a sassan Najeriya ciki har da jihar Plateu inda aka shirya gasar cin kofin Gwamna na kwallon dawaki....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.